Friday 11 July 2014

DAUKI DAYA KA BAR MINI DAYA

A wani kauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro a cikin buhu. Sai suka tsaya shawarar inda za su tafi su raba ba tare da kowa ya gansu ba. Sai daya ya bayar da shawarar a tafi makabarta.

Bayan sun isa makabarta dauke da mangoron nan, a kofar shiga sai mangoro biyu ya fado daga cikin buhun, amma saboda suna sauri kada a gansu sai suka bar su nan suka wuce cikin makabartar da sauran mangoron.

Su na shiga sai suka zube mangoron a kasa suka fara rabawa, babban ne ya ke rabo, sai ya dauki mangoro daya ya aza a gabanshi ya ce, "Ni daya" sai kuma ya dauki daya ya aza a gaban karamin ya ce, "Kai daya."

Haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye shayensa, yana zuwa dai dai kofar makabarta sai ya ji wata yar karamar murya kamar ta yara ana cewa, kai daya, ni daya, kuma anci gaba da maimaitawa. Sai kawai ya garzaya da sauri sai gidan limamin kauyen.

Yana zuwa ya same shi kofar gida yana shirin yin alwalar magariba. Ya ce, Allah gafarta malam, yau wani bakon al'amari ke faruwa a makabartar can. Na ji ana rabon matattu. Sai liman ya ce mu je in gani.

Su na zuwa, sai suka labe a bakin kofar makabartar, sai suka ji ana cewa, kai daya, ni daya, kai daya, ni daya... Can sai suka ji ance, to kai ga yawan naka nan, ni ga yawan nawa nan. Can kuma sai suka ji an kara cewa, to wadancan biyun na bakin kofar shigowa fa? Sai suka ji an ce, sai ka dauki daya ka bar mini daya.

Haba! Ai liman da mashayin nan na jin haka, sai suka ari takalmin kare, su na fadin ai mu ba matattu ba ne, tsammani suke yi da su ake, ba su san cewa yaran nan mangoron su biyu da suka fadi bakin kofa suke nufi ba.

Wai a cikinsu wa zai fi wani gudu?