Friday 11 July 2014

DAUKI DAYA KA BAR MINI DAYA

A wani kauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro a cikin buhu. Sai suka tsaya shawarar inda za su tafi su raba ba tare da kowa ya gansu ba. Sai daya ya bayar da shawarar a tafi makabarta.

Bayan sun isa makabarta dauke da mangoron nan, a kofar shiga sai mangoro biyu ya fado daga cikin buhun, amma saboda suna sauri kada a gansu sai suka bar su nan suka wuce cikin makabartar da sauran mangoron.

Su na shiga sai suka zube mangoron a kasa suka fara rabawa, babban ne ya ke rabo, sai ya dauki mangoro daya ya aza a gabanshi ya ce, "Ni daya" sai kuma ya dauki daya ya aza a gaban karamin ya ce, "Kai daya."

Haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye shayensa, yana zuwa dai dai kofar makabarta sai ya ji wata yar karamar murya kamar ta yara ana cewa, kai daya, ni daya, kuma anci gaba da maimaitawa. Sai kawai ya garzaya da sauri sai gidan limamin kauyen.

Yana zuwa ya same shi kofar gida yana shirin yin alwalar magariba. Ya ce, Allah gafarta malam, yau wani bakon al'amari ke faruwa a makabartar can. Na ji ana rabon matattu. Sai liman ya ce mu je in gani.

Su na zuwa, sai suka labe a bakin kofar makabartar, sai suka ji ana cewa, kai daya, ni daya, kai daya, ni daya... Can sai suka ji ance, to kai ga yawan naka nan, ni ga yawan nawa nan. Can kuma sai suka ji an kara cewa, to wadancan biyun na bakin kofar shigowa fa? Sai suka ji an ce, sai ka dauki daya ka bar mini daya.

Haba! Ai liman da mashayin nan na jin haka, sai suka ari takalmin kare, su na fadin ai mu ba matattu ba ne, tsammani suke yi da su ake, ba su san cewa yaran nan mangoron su biyu da suka fadi bakin kofa suke nufi ba.

Wai a cikinsu wa zai fi wani gudu?

DAN KARAMIN MUGU

Wani yaro ne babansa ya tafi da shi masallaci ranar Juma'a, suna cikin tafiya sai suka gamu da wani wada, shi ma zai shiga masallacin, sai yaron ya ce ma wadan, "Kai ma babanka ne ya zo da kai?"

Ashe wadan nan haushi ya kama shi, kuma sai aka yi katari sun yi shimfida a wuri daya. Da zarar an yi sujada, sai wada ya zabga wa yaron nan mintsini, yaro ya yi ta kara, aka rasa abin da ke faruwa.

Tun daga ranar nan, duk inda yaron ya ga wada, sai ya ce, "Lah! ga dan karamin mugun nan!" hahahaha...

Shin wai dan karamin mugun nan bafulatani ne ko kanuri?

BUZU DA BAHAUSHE

Akwai wani buzu, falke, wanda ya ke kawo dabbobi daga kasar Arewa ya kai kasar Hausa ya sayar. Duk lokacin da ya zo da dabbobin nan ya kan kwana uku ko biyar kafin ya sayar, wani lokaci ma har bakwai daya ya kan yi. Ya danganta dai da yanayin kasuwa.

To duk tsawon kwanakin da zai yi kafin ya sayar da dabbobinsa, ya kan sauka a gidan wani bahaushe ne. Bahaushen nan kuwa mutumin kirki ne, mai son karrama baki.

Kullum idan buzun nan ya dawo daga kasuwa da yamma, sai maigidan ya sa a kawo masa abinci, mai rai da lafiya, shi kuwa ya zauna ya nada iya cikinsa, har sai ya rage, yana mamakin yadda bahaushe ke kashe kudi don kawai shirya abinci irin wannan. Haka ake masa kullum har lokacin da zai koma gida.

Wata rana da buzun nan zai kawo dabbobi Hausa, sai ya zo tare da wani mutum. Bayan sun iso, an saukar da su sun huta. Da yamma ta yi kafin a kawo musu abinci, kamar yadda aka saba, sai gogan ya je wajen maigida ya ce, "Yalla, abincin nan na banza da ka ke kawo mini in kasa cinyewa, yalla na zo da namiji mai cinye shi."

Wai idan kai ne maigidan nan za ka kawo musu abincin? Ko kuwa me za ka yi wa buzun nan?

BANZA TA KORI WOFI

Wani saurayi ne da gidansu ke kusa da makabarta, kullum idan ya hawo mota ko babur baya biya, ana zuwa daidai makabartar nan sai ya ce a sauke shi, ana sauke shi sai ya nuna ai shima mataccene, fatalwa ya yi ya fito yawon shakatawa, kawai sai ya shige makabartar.

Ana cikin haka ne wata rana ya hawo babur din wani dan achaba me shegen naci, bayan sun zo daidai makabartar sai saurayin nan yace, "Tsaya na sauka anan" yana sauka sai yai kokarin shiga makabarta kamar yadda ya saba, amma sai Dan achaba ya rike shi ya ce ya ba shi kudinsa, to anan ne saurayin nan ya ce da shi shi fa fatalw ne ba me rai bane kuma gida ya kawoshi (wato makabarta).

Nan take Dan achaba ya ce to su shiga ya ba shi kudinsa. Haka kuwa aka yi, suna shiga abokin namu ya je kan wani kabari yace, "Danlami bani naira tamanin (#80) na ba wa wannan Dan achaban kudinsa", ai kafin ya gama rufe baki kawai sai suka ga wani hannu ya bullo da naira dari (#100) yace, "Karbi wannan ka ba shi, ya ba mu chanji, ni ma ragowar kudina ke nan."

Ai da Saurayin nan da Dan achaba sai kowa ya cika rigarsa da iska yayi takansa. Ashe wani Mahaukaci ne yazo ya kwanta a ciki, banza ta kori wofi ke nan.

A ganinku, tsakanin saurayin da Dan achaba wa zai fi wani gudu?

ALLAH YA SA KU MUTU

Wata rana, da yamma, wani mahaukaci ya zo zai wuce ta gaban majalisar wasu samari, sai ya dube su ya ce, Allah ya sa duk ku mutu! Sai kow ya kyale shi. Sai ya kara cewa, Allah ya sa duk ku mutu! Suka kara yin banza da shi. Da mahaukacin ya ga babu wanda ya tanka masa, sai ya wuce ya na ta dariya.

Bayan ya wuce sai samarin nan suka ci gaba da hirarsu, su na cewa, mahaukacin banza, in ban da mahaukaci wa ke so ya mutu?

Ran nan kuma sai mahaukacin nan ya kara dawowa wurin samarin nan zai wuce, sai ya dube su ya ce, Allah ya sa duk ku shiga Aljanna. Sai duk suka amsa da sauri, Amin, Amin, Allah ya sa. Mahaukaci ya dube su ya fashe da dariya ya ce mahaukatan banza! Kun taba ganin an shiga Aljanna ba a mutu ba? Ya wuce ya na ta dariya, ya barsu nan cikin tunani.

To wai me ya sa muke tsoron mutuwa ne? Hala bamu shirya mata ba? To me ya ke hana mu shirya ma zuwanta? Don haka kowa ya yi wa kansa wa'azi!

Allah ya bamu ikon karba kira cikin shiri.

KAMSHIN ALJANNA

A kasuwar duwatsu masu daraja akwai wani tsoho mai gyaran karyayyun zobuna da sarkoki da sauran abubuwan da aka yi da duwatsu masu daraja kuma yana sayarwa.

Wata rana yana cikin shagonsa, sai wani mutum mai ban mamaki ya shigo ya kawo masa gyaran zobensa. Abin mamakinsa kuwa shi ne duk gashin da ke jikinsa fari ne tas, sannan kuma tufafin jikinsa su ma farare ne, haka hularsa, kai har takalmin mutumin nan farare ne tas, sai daukar ido su ke yi, ga kamshi sai tashi ya ke yi daga jikin mutumin.

Mai sahago ya ba shi wuri ya zauna, shi kuma ya soma gyara ke nan sai ga wasu mutane biyu, mata da miji, sun shigo suka dudduba sai suka ce ya taso ya ba su kaya. Sai ya ce, "Don Allah ku jira na sallami wannan bawan Allan." Ya nuna musu mutumin nan.

Ga mamakinsa sai ya ga sun canza masa kallo, suka dudduba ko'ina, suka yi kamar ba su ga bakon mutumin nan ba. Mai shago ya ga suna magana kasa-kasa, amma bai iya jin me suke cewa. Daga karshe sai suka yi waje da sauri, shi kuma ya ci gaba da aikinsa.

Can kuma sai ga wani mutumin ya shigo shagon a uzurce, ya ce, "Dattijo don Allah sauri na ke yi, dan gyara mini sarkar nan yanzu." Sai mai shago ya ce, "To dan jira ni kadan na karasa wa wannan bawan Allan aikinsa." Sai ya ga mutumin sai waige-waige ya ke yi, ya ce, "Haba dattijo, ni dai ban ga kowa ba, ko dai tsufa ne ya fara taba ka?" Sai ya yi waje abinsa.

Da mutumin nan mai fararen kaya ya ga haka, sai ya ce, "Malam ni fa ba kowa ne ke iya ganina ba, don ni ba mutum ba ne, ni mala'ika ne, na zo ne na yi maka albishir saboda irin yadda kake gudanar da harkokinka tsakani da Allah, shi ya sa Allah ya tanadar maka Aljanna ta musamman. Yanzu haka daga cikinta na fito ka ga wannan ma daga can na zo da shi." Sai ya fito da wani kyalle mai kyau, mai shago bai taba ganin kyalle mai kyawunsa ba ya ce masa, "Sunsuna ka ji yadda kamshin Aljannarka ya ke."

Da tsoho ya ji labarin Aljannah, ai cikin gaggawa ya amshi kyalle ya kai hanci ya shasshaka shi da karfi. HABA AI SAI FARKAWA YA YI YA GAN SHI A ASIBITI.

Ashe mutanen nan duk 'yan 419 ne suka yiwo shiri don su cuce shi. Allah ka tsare mu da sharrin 'yan damfara, Amin.

JAKI DA KWIKWIYO

Wani manomi ne yake da jakinsa da yake hawa kullum idan zai je gona. Manomin nan na kula da jakinsa matuka. Ana ba shi abinci mai kyau da ruwa, kuma kullum ana share masa wurin kwanciyarsa.

Ran nan bayan manomi ya dawo gona da jaki, ya zauna yana hutawa, jaki kuwa yana kwance can gefe cikin inuwa, sai ga wani dan kwikwiyo ya zo gaban manomi yana 'yan tsalle-tsallensa na wasa yana lasar kafafun manomi. Manomi kuwa yana kallonsa yana dariya, har dai dan kwikwiyo ya fada bisa jikinsa.

Manomi ya rika shafa jikin dan kwikwiyo cikin jin dadi, ya sa hannunsa cikin aljihu ya fito da wani abinci ya ba dan kwikwiyo. Ashe duk abin nan da ake yi jaki da ke can gefe kwance yana kallo. Shi ma sai ya tashi yana tsalle-tsalle, kamar yadda ya ga dan kwikwiyo na yi, wai shi ma ya burge mai gidansa.

Da manomi ya ga haka sai ya fara dariya, jaki kuwa ganin ya fara shiga gun mai gida, sai ya matso ya dora wa mai gida kafafunsa, wai shi ma zai hau jikinsa kamar yadda dan kwikwiyo ya yi. Ko da yaran mai gida suka ga jaki na shirin lahanta mai gida, sai suka taso masa da kulake, suka yi ta dimar shi. Jaki ya gudu yana cewa: " Ashe dai inda wani ya yi rawa aka ba shi kudi, idan wani ya yi duka zai sha."

KWADI DA SARKINSU

Wasu kwadi ne suke zaune a cikin wani tabki cikin jin dadi da walwala, ba abin da suka nema suka rasa, idan sun gaji da wasansu cikin ruwa sai su tsallaka kan tudu su sha iska. Ba su damuwar kowa, kuma babu wani abu da yake damun su.

Suna nan haka sai wasu daga cikinsu suka ce, ina amfanin zamanmu haka babu wani Sarki da zai rika mulkinmu, ba mu da wasu dokoki da za su tafiyar da tsarin rayuwarmu. Allah kuwa ya amshi addu'arsu!

Ana nan wata rana sai wani dan guntun reshen bishiyar da take bakin tabkin ya karye, ya fado kwatsam a gefen tabkin. Kwadi suka tsorata suka fada ruwa da gudu. Sai wasu daga cikinsu suka ce ai Sarkin da suke roko a turo musu ne Allah ya turo musu.

Kwadi na cikin ruwa suna jira su ji irin dokokin da Sarki zai shata musu, suka ji shiru, su kuma suna jin tsoron su matsa kusa da shi. Ana nan dai har wani mai karfin hali daga cikinsu ya matsa kusa da reshen itacen nan da ya fado, sannu-sannu har ya kai ga taba shi, icce bai motsa ba, har ya hau kansa, yana rawa, itace dai bai motsa ba. Da saura suka ga haka, sai duk suka fito suka haye kan reshen itace. Sai ya kasance koyaushe nan ne wurin zaman kwadi tare da sabon Sarkinsu.

Sai dai kwadi ba su yi murna da wannan Sarki da aka turo musu ba, suka nuna sun fi son Sarki mai rai, mai motsi, wanda zai rika shata musu dokoki, kuma ya shimfida mulkinsa.

Wannan buri na kwadi ya sa Allah ya yi fushi da su. Kwaram ran nan sai ga wani zalbe zai wuce ta wurin, sai ya ga kwadi da yawa bakin tabki, shi ke nan abin nema ya samu, dama wurin neman abinci zai tafi. Sai ya tsaya bakin tabkin nan ya rika kama kwadi yana cinyewa.

Da kwadi suka ga zalbe ya dame su da kisa haka, ya hana su sakat, sai suka ce wannan wane irin Sarki ne aka turo mana. Mu dai mun fi son zamanmu na da. DA MULKIN ZALUNCI GWAMMA ZAMA BABU SARKI!

Thursday 10 July 2014

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 7

Da gari ya waye, Ali Baba ya fito farfajiyar gidan domin su gaisa da bakonsa, ga mamakinsa sai ya ga kofar dakinsa a bude, babu bako babu alamunsa, amma kuma ga dabbobinsa nan da kuma hajarsa ta mai. Yana nan tsaye yana mamakin inda bakonsa ya shiga, sai ga kuyangarsa Murjanatu ta fito, ta durkusa ta gaishe shi.

Ya tambaye ta, ko ta ji motsin bakonsa? Domin tagar dakinta na kallon farfajiyar gidan ne, duk wani motsi da za a yi a farfajiyar gidan Murjanatu za ta iya ji daga cikin dakinta. Ta ce da Ali Baba, "Maigida zo ka duba da idonka, ka kara yi wa Allah godiya, da ya kubutar da kai." Ta ja shi har zuwa wurin da jakunkunan mai suke, ta ce ya bude daya da kansa ya ga abin mamaki.

Ali Baba ya bude jakar mai daya, sai ya ga mutum a ciki, rike da takobi. Ya juya zai gudu cikin tsoro, Murjanatu ta dakatar da shi. Ta ce, "Wannan mutum da kake gani ba zai iya cutar da kai da komai ba domin kuwa ba shi da rai. Mutum talatin da bakwai ne, duk Allah ya ba ni nasarar kashe su da tafasasshen mai." Ta kwashe labarin abin da ya faru duka tun daga lokacin da ta ga ana yi wa gidansu lamba, da kuma yadda ta zo dibar mai a cikin hajar bako, ta gane mutane ne a ciki, da yadda ta kona su da mai, da kuma yadda ta ga shugaban barayi ya bude gida cikin dare ya arce, da ya gano cewa an kashe masa mutane.

Ali Baba ya yi mamaki a kan hikima da kuma dabara ta wannan yarinya, gayar mamaki. Ya gode mata, godiya mai yawa, kuma ya yi mata abishir da wata kyauta mai tsoka, amma bai fada mata ko mene ne ba. Ya tura ta ta kira masa wani bawansa mai suna Abdallah.

Da Abdallah ya zo, Ali Baba ya fada masa abin da ke faruwa. Ya ce yana so su tafi lambun da ya ke cikin gidan su gina katon rami mai fadi da zurfi, wanda zai iya daukar barayin nan duka, su rufe su ciki. Ali Baba ya taimaka wa bawansa Abdallah suka gina katon rami, Allah ya taimake su akwai danshi a cikin lambun, saboda haka ba su sha wata wahala ba wurin haka ramin.

Suka rika ciccibo gawar barayin nan, daya bayan daya, suna jefawa cikin ramin duk da jakunkunan da suke ciki, har suka jefa su duka. Suka mayar da kasa suka rufe. Ali Baba ya gargadi bawan nan, duk da yake ya san amintacce ne, a kan kada ya kuskura ya yi wannan zance da kowa a waje. Jakan barayin nan kuwa, sai Ali Baba ya rika dibar biyu, uku, yana tura Abdallah da su kasuwa yana sayar masa, tunda ba wani amfani zai yi da su ba, har suka kare.

Shugaban barayi kuwa da ya gudu daga gidan Ali Baba, sai ya koma maboyarsu a cikin daji. Ba da jimawa ba, kadaici da kuma tsoro suka lullube shi, ya ji kwata-kwata ba zai iya zama shi kadai a cikin daji ba. Saboda haka sai ya debi wani abu daga cikin dukiyar nan, ya yi shiri kamar wani bakon alhaji, ya koma cikin gari.

Da ya isa cikin gari sai ya tasar wa fada. Aka yi masa iso gun Sarki, ya ce shi bako ne, sunansa Koja Husaini, yana so ya zauna a cikin wannan gari idan Sarki ya yarda, idan ma zai samu gida na siyarwa, to zai siya ya zauna a ciki. Sarki ya sa dillalai suka nemo wa Koja Husaini gida, aka yi ciniki ya biya. Kwamfa! Ashe gidan kuma yana makwaftaka ne da tsohon gidan Ali Baba wanda ya tashi a ciki, ya koma gidan Kasim, wanda kuma yanzu babban dansa ne, saurayi dan kimanin shekaru ashirin da uku, a ciki.

Koja Husaini ya tare cikin sabon gidansa, lokaci-lokaci kuma yakan koma maboyarsu ya debo wani abu daga cikin dukiyarsu, wadda yanzu ta zama mallakarsa shi kadai. Amma ya kan yi taka-tsan-tsan duk lokacin da zai tafi, domin kada ya ja hankalin mutane su fara zarginsa. Kullum zuciyarsa cike take da tunanin hanyar da zai bi ya kashe Ali Baba.

Sannu a hankali Koja Husaini ya fara sabawa da makocinsa, dan Ali Baba, duk da yake ba sa'arsa ba ne, har ta kai ga wani lokaci suna zaunawa su yi ta hira a tsakaninsu.

Ana nan wata rana sai Ali Baba ya kawo wa dansa ziyara a gida, a lokacin kuma Koja Husaini na zaune a kofar gidansa, karkashin wata bishiya, yana hutawa. Da ganinsa, nan take Koja Husaini ya shaida shi. Ali Baba ya shige gidan dansa, bai ko lura da wani mutum ba, ballantana ya lura da ana kallonsa.

Bayan wani lokaci, Ali Baba ya fito daga gidan ya yi tafiyarsa. Ba a dade ba kuma sai ga dansa ya fito, da ya ga Koja Husaini zaune a kofar gidansa, sai ya nufi can domin su yi hira. A cikin hirar tasu ne Koja Husaini ya fahimci cewa wannan yaro, wanda ya zama tamkar abokinsa a halin yanzu, dan Ali Baba ne, babban makiyinsa a duniya. Don haka sai ya raya a zuciyarsa, bari ya ja shi a jika, wata kila ta sanadiyarsa zai cimma burinsa na kashe Ali Baba.

Tun daga wannan rana sai alakar Koja Husaini da Dan Ali Baba ta dauki sabon salo. Koyaushe Koja Husaini ba ya da wani aboki da ya wuce Dan Ali Baba, ya yi ta jan sa a jika har suka shaku da juna suka zama tamkar abokai sa'o'in juna.

Ina ya Allah, babu ya Allah! Ana nan sai matar Ali Baba ta haihu. Tun kafin ranar suna Ali Baba ya shirya wata 'yar gajeruwar liyafa ta cikin gida, watau iyalansa da barorinsa kawai. Da Dan Ali Baba zai je wurin liyafar sai ya gayyaci babban abokinsa, Koja Husaini, domin ya raka shi. Koja Husaini ya yi matukar farin ciki a ransa, damar da yake ta faman jira kwana da kwanaki yanzu ta samu. Idan suka tafi, zai yi iyakar kokarinsa ya kebe da Ali Baba wani wuri, inda babu kowa, ya kashe shi ya gudu, lokacin da duk hankulan iyalansa suke wurin liyafar. Sai ya dauki wata sharbebiyar wuka ya sulle ta a cikin rigarsa, suka tafi.

Ko da suka isa gidan, komai ya kankama. Dan Ali Baba ya gabatar da abokinsa ga mahaifinsa, sannan suka sami wuri suka zauna. Duka-duka wurin liyafar bai wuce mutum biyar zuwa shida ba; Ali Baba da matarsa, Dan Ali Baba da abokinsa Koja Husaini, Abdallah bawan Ali Baba, sai kuma yarinya Murjanatu da take ta faman kawo kayan ciye-ciye da shaye-shaye.

Murjanatu na cikin rarraba abinci ga mahalarta liyafa har ta zo kan Koja Husaini. Tana ganinsa, nan take kwakwalwarta, mai kama da kwamfuta, ta gane shi. Shugaban barayin nan ne ya sake dawowa. Tabbas wannan zuwan ma, akwai manufar da ya zo da ita, ba liyafar ce ta kawo shi ba. Ta kanne abin a cikin ranta, ba ta ce komai ba, ba ta kuma nuna alamun komai ba, tana tunanin hanyar da za ta yi maganin wannan barawo.

Bayan liyafa ta kankama, kowa ya fara motsa bakinsa da abin da aka tanadar. Tuni kuma Murjanatu ta gano wata dabara da za ta kashe wannan barawo. Ta rada wa bawan nan Abdallah, ya dauko dundufarsa ya fara kida ita kuma za ta yi rawa, kamar yadda suke yi wa Ali Baba a duk lokacin da yake bukatar nishadi. Abdalla ya jawo dundufarsa ta kida, ya fara kadawa a hankali, dama kuma gwanin kida ne, ita kuma Murjanatu ta tashi ta fara taka rawa, abin gwanin ban sha'awa.

Al'adar garin ce, idan mace tana rawa a cikin maza, ta kan rike wata 'yar karamar wuka a hannunta. Idan ta yi rawa, ta yi juyi, sai ta zo gaban mutum ta daga wukar nan kamar za ta daka masa ita a zuciya, sai ta juya wukar ta daka masa marikin wukar. Sai a yi tafi, a yi shewa, ta haka ake gane namiji mai tsoro da kuma jarumi. Duk kasar kowa ya san da wannan al'ada, hatta Koja Husaini ya san da haka.

Saboda haka lokacin da Murjanatu za ta fara rawa, sai ta dauko 'yar karamar wuka ta rike a hannunta, tuni ta ayyana abin da za ta yi a cikin ranta. Ta fara rawa tana juyi, ta zo kan mai kida, Abdallah, ta daga wukar kamar za ta daba masa ita, sai ta daba masa kotarta, aka yi tafi. Ta wuce wurin Dan Ali Baba, ta yi kamar yadda ta yi wa Abdallah, ta wuce. Ta je kan Shugaban barayi, ta daga wukar nan, ta tattara iyakar karfinta a hannunta mai wukar ta kirba masa ita a kahon zuciya. Nan take barawo ya fadi kasa yana shure-shure har ya mutu.

Ko da Ali Baba da dansa suka ga wannan danyen aiki da Murjanatu ta aikata, wanda ba su san dalili ba, sai suka taso mata, hankalinsu a tashe, suka far mata da fada, don me za ta kashe bakon da suka gayyato, laifin me ya yi mata. Murjanatu ta dakatar da su, sannan ta bayyana musu ko wane ne wannan bako, sannan ta ce musu, "Duk da yake ban san manufar da ya shigo da ita wannan gida ba, amma na tabbata manufarsa ba ta alheri ce ba."

Da suka duba jikin shugaban barayi, sai suka samu sharbebiyar wuka sulle a cikin rigarsa. Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Murjanatu ta kubutar da rayuwar Ali Baba daga halaka. Saboda haka yanzu ne zai sanar da ita albishirin da ya boye mata a cikin zuciyzrsa, wanda kuma ya taba furta mata.

Ali Baba ya dubi Murjanatu ya ce, "Daga yau na 'yanta ki, kin zama 'ya mai cikakken iko, kuma idan kin yarda ina so ki amince da dana ya zama mijinki." Sannan ya juya wurin dansa ya ce da shi, "Ya kai dana, na san da cewa ba za ka ki amincewa da zabina ba, ka amince na aura maka Murjanatu domin na tabbata ta dace da kai, kuma ba domin ita ba da wannan abokin naka ya sami galaba a kaina, dama ya yi kokarin yin abota da kai ne domin ya samu ya kashe ni. Na tabbata da bukatarsa ta biya, kai ma ba zai bar ka ba. Don haka wannan yarinya ita ce sanadiyar kubutarmu gaba daya."

Murjanatu da Dan Ali Baba suka amince da junansu. Bayan 'yan kwanaki aka daura musu aure, aka sha biki aka watse, mutanen gari suka yi ta sa albarka, a kan wannan karimci da Ali Baba ya yi wa yarinya Murjanatu, ga ta baiwa amam ya 'yanta ta kuma ya aurar da ita ga dansa, da ma yarinya ce mai ladabi. Duk mutanen gari babu wanda ya san abin da ya faru.

Ali Baba bai kara komawa maboyar 'yan fashin nan ba, domin yana gudun ya hadu da sauran barayin nan biyu da bai san abin da ya same su ba. Da aka shekara ya ga babu wata barazana da barayin nan suka kara yi masa, ran nan sai ya shirya ya faki idon mutane ya dare saman dokinsa, ya nufi dajin. Ya debo dukiyar ya aza kan dokinsa ya hawo ya dawo.

Haka Ali Baba ya ci gaba da zuwa dajin nan daga lokaci zuwa lokaci, yana debo dukiyar da barayin nan suka tara yana kawo wa gida, sai dai duk lokacin da ya je yakan yi sauri ya diba ya dawo don tsoron kada sauran barayin biyu su tarar da shi. Ya ci gaba da yin haka tsawon shekaru, ya kwashe dukiyar duka ya kawo gida, kuma yana ci gaba da kasuwancinsa a kasuwa, don haka babu wanda ya san sirrunsu. Ya zamana babu mai arziki duk fadin kasar kamar Ali Baba.

Yayi zamansa shi da iyalinsa cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai rabawa ta zo ta raba su.

KARSHE.

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 6

Lokacin da shugaban barayi ya koma cikin daji wajen 'yan uwansa, ya shaida musu cewa ya gane gidan Ali Baba. Dabarar da za su yi su kashe shi, ba tare da sun ja hankalin jama'ar garin ba ita ce, yana so su tafi inda suke boye dabbobinsu, su zo da jakai goma sha tara, sannan su shiga cikin kasuwar garin su siyo jakunkuna na fata, wadan da ake dura wa mai, manya-manya wadan da mutum zai iya shiga cikinsu, guda talatin da takwas.

Ya ci gaba da cewa, "Idan muka hada wadan nan dabbobi da kuma jakunkunan dura mai, kowane mutum daya zai shiga cikin jaka daya da takobinsa, jaka dayar da za ta rage, zan dura man girki a cikinta. Zan dora ku gaba daya a kan jakai, duk mutum biyu jaki daya. Mutum na karshe zan dora shi tare da jakar da take da mai. Ni kuma zan yi shigar farke, na kora jakunan nan zuwa cikin gari. Zan dakata har zuwa faduwar rana sannan na shiga cikin gari, na je gidan mutumin na shaida masa cewa ni farke ne, na kawo man girki ne, ga shi dare ya yi ban samu shiga kasuwa ba. Ina so ya taimaka mini da wurin da zan sauke kayana a gidansa, idan gari ya waye sai na dauka na shiga kasuwa."

Shugaban barayi ya ci gaba da cewa, "Na san cewa zai yarda da bukatata. To, zan sauke ku na bar ku a wajen. Idan na ji gari ya yi shiru, kowa ya yi barci, zan zo na rika taba kowace jaka, duk wanda ya ji na taba jakarsa to sai ya fito, lokaci ya yi ke nan da za mu aikata abin da za mu aikata. Mu kashe shi da iyalinsa duka, sannan mu kwashe dukan dukiyar da take gidan, mu dora wa dabbobin nan mu koro su mu dawo. Ina fatar kun fahimce ni."

Sauran barayi suka ce sun fahimta. Ya rarraba su, ya aika wasu su zo da jakai, sannan ya aika wasu su tafi cikin gari su siyo jakunan dura mai da kuma man da zai cika jaka daya. Duka suka tafi neman abin da shugabansu ya umurce su da samowa.

Bayan kwana biyu barayin nan suka gama shirinsu tsaf. Kowane barawo ya shiga cikin jaka daya rike da takobinsa. Da suka gama shiga gaba daya. Shugaban barayi ya yi sadi da su a kan jakai, duk jaki daya ya dauki barawo biyu a cikin jaka. Jaki na karshe ya dauki barawo daya da jakar mai.

Shugaban barayi ya canja kamanninsa, ya yi shiga kamar farke, ya kora jakai dauke da barayi suka nufi cikin gari. Bayan tafiyar wani dan lokaci, suka isa bakin gari, dab da rana za ta fadi. Da shigarsu cikin gari, shugabn barayi ya kora dabbobin nan ya nufi gidan Ali Baba da su. Yana isa kuwa ya yi sa'a da Ali Baba ya dawo daga kasuwa, zai shiga gida ke nan, barawo ya dakatar da shi.

Bayan sun gaisa, sai barawo ya ce wa Ali Baba, "Ni farke ne, na zo da man girki ne domin kai wa kasuwa na sayar, ga shi dare ya yi mini ban samu shiga kasuwar ba, ko zan samu alfarmar masauki a wurinka da kuma wurin da zan sauke kayana kafin gobe da safe na shiga kasuwa?"

Ali Baba ya ce, "Wa zai ki bako? Ai bako rahama ne. Babu komai, shigo da kayanka daga ciki ka sauke kafin Allah ya kai mu gobe. Zan dawo na nuna maka dakin da za ka kwana idan ka gama sauke kayan." Barawo ya yi ta godiya, kamar mutumin kirki. Ali Baba kuwa ya wuce cikin gida, ya bar barawo ya na sauke kayansa a farfajiyar gidan.

Da Ali Baba ya shiga cikin gida, sai ya fada wa matarsa da kuyangarsa Murjanatu cewa ya yi bako. Ya ce, "Farke ne ya zo da man girki zai kai kasuwa ya siyar amma dare ya yi masa, don haka zai kwana a nan gidan tare da kayansa zuwa gobe da safe. Yanzu zan fita zuwa farfajiyar gidan mu kara gaisawa da shi, a kai mini abinci na can, za mu ci tare." Suka amsa masa da to. Ya fita.

Ko da ya fita ya tarar da shugaban barayi ya gama sauke kayansa. Ali Baba ya nuna masa dakin da zai kwana. Barawo ya kara yin godiya, sannan ya ce wa Ali Baba yana so ya nuna masa cikin gari domin bude ido, tun da shi bako ne. Ali Baba ya ce masa to, amma ya dakata sai sun ci abinci tukuna.

Murjanatu ta kawo musu abinci, har ta juya za ta tafi sai Ali Baba ya ce da ita, "Idan mun gama cin abinci za mu shiga cikin gari ni da bakona, akwai kifi na nan na siyo, ina so ki soya mana shi kafin mu dawo daga cikin gari." Murjantu ta amsa cikin girmamawa, ta tafi.

Bayan Ali Baba da barawo sun gama cin abinci, sai suka tashi suka nufi cikin gari. Ita kuma kuyanga Murjanatu ta dauko kifi ta nufi dakin dafa abinci domin soyawa kamar yadda aka umurce ta. Bayan ta hura wuta, ta dora tasar suya, sai ta jawo jakar da ake ajiye mai a ciki, sai ta ji ta kwambar babu komai a ciki. Ashe ta manta sauran man ne ta yi abinci da shi. Ga shi dare ya yi ballantana a tafi kasuwa a siyo. Nan take sai ta tuna, "Af! Shin bakon maigida mai ne ya zo da shi domin siyarwa kasuwa ba? Bari na je wurin da ya sauke man, na debo wanda zan soya musu kifin da shi, alabashi idan maigida ya dawo sai in fada masa, sai ya saye jakar man da na diba gaba daya."

Ta dauki abin dibar mai ta nufi inda shugaban barayi ya sauke kaya. Tana zuwa sai ta taba jakar mai daya za ta bude, sai ta ji an ce, "Lokaci ya yi ne?" Sai abin ya bata mamaki, nan da nan ta gane abin da ake shirin kulla wa maigidanta, sai ta canja murya kamar namiji ta ce, "Da saura!"

Ta nufi wata jakar za ta buda, sai ta ji an ce, "Lokaci ya yi ne?" Ta kara canja murya ta ce, "Da saura!" Sai da ta bi duka jakunkunan nan guda talatin da bakwai, ta gane duka mutane ne a cikinsu, sai guda daya ce kurum ta ke dauke da mai. Ta ciccibi jakar da take da mai, ta nufi dakin girki.

Da isarta dakin girki, sai ta sauke tasar suyar kifi ta dora babbar tukunya, ta juye man nan gaba daya a cikin tukunyar. Ta tafasa man sosai har sai da ya tafasa. Ta diba yadda za ta iya dauka, ta dauki shantu ta tafi wurin barayin nan. Idan ta je ga jaka sai ta tura shantu a ciki, ta dura tafasasshen mai a cikin jakar, tun barawo na motsi har sai ta ji ya yi shiru, ya mutu. Haka ta bi su daya bayan daya, tana kashe su da tafasasshen mai, har ta kashe su duka. Sannan ta soya kifin da aka ce ta soya.

Lokacin da Ali Baba da shugaban barayi suka dawo daga yawo cikin gari, Murjanatu ta kawo musu kifi suka ci. Da suka gama suka yi sai-da-safe da juna, barawo ya shige dakinsa, bai san abin da ake ciki ba, shi ma Ali Baba ya shige cikin gida.

Ita kuwa Murjanatu da ta shiga dakinta ta rufe kofa, sai ta bude taga tana kallon abin da zai faru a farfajiyar gidan idan shugaban barayi ya gane an kashe masa mutane.

Can da dare ya tsala, gari kowa ya yi tsit, sai Murjanatu ta ga shugaban barayi ya bude dakinsa a hankali ya fito, ya nufi inda jakunkunan mai suke. Ta ga ya taba daya, ya jira bai ji motsi ba. Ya kara taba wata, babu motsi. Ya bi su gaba daya ya taba, babu mai motsi. Sai ya bude daya, domin ya ga ko barci ne ya dauke su. Sai Murjanatu ta ga ya ja da baya cikin alamun jin tsoro. Daga nan sai ta ga ya yi sauri ya nufi kofar fita daga gidan, ya bude, ya arce.

Murjanatu ta mayar da tagar dakinta ta rufe, ta tabbata cewa maigidanta ya tsallake wannan tarko, sai dai ba ta san da wane shiri wancan barawon da ya tsallake zai dawo ba, ko wane irin tarko zai sake kafa wa Ali Baba? Ta kwanta kan gadonta tana jiran gari ya waye ta fada wa Ali Baba halin da ake ciki.

Za mu ci gaba....

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 5

Al'adar garin ce idan mutum ya mutu, 'ya 'yansa ne za su gaji dukan dukiyarsa, idan kuwa ba shi da 'ya 'ya, to 'yan uwansa ne za su gaje shi, idan babu kuma sai matarsa ta gaje shi, idan ba shi da mata sai a saka dukiyarsa a baitulmali.

Bayan mutuwar Kasim, kasancewar ba shi da 'ya 'ya, sai Ali Baba ya gaji dukan dukiyarsa, da gidansa da kuma kuyangar nan tasa mai tsananin hikima, watau Murjanatu. Ali Baba ya kwashe dukan dukiyar da ya samu daga taskar 'yan fashin nan ya koma gidan Kasim tare da matarsa. Ita kuma matar Kasim ta koma gidan mahaifinta.

A cikin wannan halin ne barawon nan ya hilaci dattijo Baba Mustafa har ya kawo shi gidan da Ali Baba ya ke ciki da matarsa da kuyangarsa. Kuma ya yi wa gidan 'yar alama da bakin fenti yadda idan suka dawo cikin dare tare da sauran barayin za su yi saurin shaida gidan.

Bayan barawo ya koma wurin 'yan uwansa, cike da farin cikin gane gidan Ali Bab, ya shaida musu cewa bukata ta biya. Barayi suka yi murna da wannan labari. Babban su ya ce, "Kowa ya zauna cikin shiri, domin yau cikin dare za mu tafi mu kashe wannan mutum, sannan mu kwashe dukan dukiyar da muka samu a cikin gidansa." Barayi duka suka shirya suna jiran dare ya yi.

Ashe kuma bayan tafiyar barawo da Baba Mustafa daga kofar gidan Ali Baba, Murjanatu ta fito domin ta kai sako wani gida. Bayan ta dawo, har za ta shiga gida, sai ta kyalla ido ta ga an yi wata 'yar alama da bakin fenti a jikin kofar gidansu. Ta duba kofar makwabtansu ba ta ga irin wannan alama ba. Ta kuma duba wani gidan, ba ta ga wannan alama ba, ta sa hannu wai ta goge alamar, amma ta ki goguwa. Sai jikinta ya ba ta lalle wannan alama da aka zana a kofar gidansu akwai wata manufa a ciki, ruwa ba ya tsami banza.

Murjanatu ta shiga gida ta samo bakin fenti, ta bi dukkan kofofin gidajen makwabtansu ta yi musu irin 'yar alamar da ta gani a kofar gidansu. Ta ja bakinta ta tsuke, ba ta fada wa kowa ba.

A cikin daji kuwa, barayi sun shirya tsab domin tunkarar gidan Ali Baba, Da lokaci ya yi, suka shirya suka nufo gari. Da suka iso bakin gari, sai suka dakata sai da dare ya raba tsakiya, ba a jin motsin komai a cikin garin, sannan suka shiga.

Barawon da ya gane gidan yana gaba suna biye da shi har suka iso unguwar da gidan Ali Baba ya ke ciki. Da zuwansu, sai suka shiga haska fitulu a kofar gidajen domin gano gidan da barawo ya yi wa lamba. Can sai wani daga cikinsu ya ce, "Ga alamar nan a jikin kofar wancan gidan." Wani kuma ya ce, "A'a, ga gidan nan." Can sai kuma wani ya kyalla ido ya ga alamar a jikin kofar wani gidan dabam.

Da barayin nan suka duba da kyau, sai suka ga ashe duka gidajen unguwar an yi musu lamba. Sai shugaban 'yan fashi ya dubi barawon da suka aiko ya ce, "Sai ka nuna mana gidan da ka gano."

Barawo cikin kaduwa ya ce, "Wallahi ni gida guda na yi wa lamba, ban san me ke faruwa ba."

Shugaban barayi ya ce, "Wane ne daga cikinsu ka yi wa lamba?"

Barawo ya duba, ya kara dubawa, ya kasa gane gidan da Baba Mustafa ya nuna masa. Sai ya ce, "Wallahi ba zan iya shaida shi ba a halin yanzu."

Shugaban barayi ya fusata ya ce, "Ka san ba za ka iya gane gidan ba ka sa muka zo, muka yi wahalar banza, za mu koma a banza a wofi? Lalle hukunci zai hau kanka." Ya ba da umurni aka daure wannan barawo a kan dokinsa, suka kora shi suka nufi cikin daji, wurin maboyarsu.

Da suka isa wurin da dutse ya ke, suka bude shi suka shiga daga ciki. Shugaban 'yan fashi ya sa takobinsa ya dauke kan barawon nan da ya kasa gane gidan Ali Baba. Sannan ya juyo ga sauran barayi ya ce,"Wa zai faranta mini rai, ya shiga cikin gari ya gano mana gidan mutumin nan, ni kuwa in saka masa da abinda duk ya ke bukata?"

Duk barayin nan suka yi jim, can sai wani ya yunkuro daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma ba zan dawo ba sai na gano takamaiman gidan wannan mutumin, idan kuma ban gane ba na yarda a zartar da hukuncin kisa a kaina, kamar yadda aka yi wa na farko."

Barawo ya yi shiri, ya canja kamanninsa kamar wani mutumin kirki, ya nufi cikin gari. Da ya isa cikin gari, sai ya tasar wa rumfar Baba Mustafa, baduku. Ya same shi zaune yana dinkin wata jakar fata.

Barawo ya yi amfani da dabarar da abokinsa na farko ya yi, ya ja hankalin dattijo da kudi, har ya kai shi dai dai kofar gidan Ali Baba. Bayan da ya sallami dattijon, sai ya dauko jan fenti a cikin jakarsa, ya sami wani wuri a jikin gidan, wanda ba duka idon mutum zai yi saurin kaiwa ga wurin ba, ya yi 'yar alama wadda za ta sa ya gane gidan.

Bayan ya tafi, sai Murjanatu ta fito zuwa wurin da aka aike ta. Bayan ta dawo, kafin ta shiga gida sai kuwa idonta ya kai ga alamar da barawon nan ya yi da jan fenti. Ta tsaya tana tunanin shin wai me ake nufi da wadan nan alamomi da ake yi musu a jikin gida? Ta je ta samo kalar fentin, ta bi dukan gidajen makwabtansu ta yi musu irin wannan 'yar alamar. Ta shiga gida ba ta fada wa kowa ba.

Shi kuwa barawo da ya koma sai ya shaida wa shugabnsu cewa ya gane gidan, don haka su shirya da dare su shiga gari su kashe mai gidan sannan su kwashe dukan dukiyar da suka samu a cikin gidan.

Da lokaci ya yi, barayi suka shirya suka shiga cikin garin da dare, lokacin kuwa duk mutane kowa ya yi barci, suka tasar wa unguwar da Ali Baba ya ke da iyalinsa. Da isarsu sai shugabansu ya ce da barawon nan, "Maza nuna mana gidan mu aikata abin da ya kawo mu, mu juya kafin gari ya waye."

Barawo ya haska fitilarsa a jikin gida na farko, dai dai inda ya san ya yi alama, sai kuwa ga 'yar alamar da jan fenti. Har za su balle gidan su shiga, sai shugabansu ya ce, "Bari mu fara tabbatar wa da kanmu cewa wannan shi ne gidan da muke nema, kada a sami kuskuren da aka samu jiya, ku tafi ku haska sauran gidajen, idan babu wani gida mai irin wannan alama, to wannan shi ne gidan da muke nema."

Sauran barayi suka warwatsu cikin unguwar, duk gidan da suka haska fitilarsu sai su ga irin wannan alama a jiki. Suka zo suka fada wa shugabansu. Shugaban ya tambayi barawon ko zai iya gane gidan a cikin sauran gidajen da suke da alama iri daya? Barawo ya ce ba zai iya ba.

Suka koma maboyarsu. Shi ma wannan barawo aka zartar masa da hukuncin kisa. Da shugabansu ya ga cikin dan kankanin lokaci ya yi asarar mutum biyu daga cikin yaransa, sai ransa ya baci, ya yi fushi, fushi mai tsanani. Ya yi rantsuwa da abin da zai kashe shi cewa, shi da kansa zai shiga gari ya gane ainihin wannan gida da suke nema, wanda ya yi sanadiyyar rasa yaransa biyu. Lalle mai wannan gida zai dandana azaba mai tsanani kafin su kashe shi.

Washe gari shugaban barayi ya yi shiri da kansa ya shiga gari. Ya yi amfani da dabarar da barayin nan biyu suka yi amfani da ita, ta saye dattijo baduku, watau Baba Mustafa da kudi.

Da suka zo kofar gidan, shugaban barayi ya sallami dattijo. Ya dubi gidan da kyau tun daga kasa har bisa, ya yi murmushi ya ce a ransa, "Yaro dai yaro ne, in ba halin yarinta ba mene na abin yi wa wannan gida alama? Wannan makeken dutsen da ya ke kwance gab da kofar shiga gidan ai ya isa alamar da za a gane gidan, ko ba shi ba ma, waccan tsagawar da bangon gidan ya yi ita ma alama ce babba ta gane gidan." Ya sake yin murmushi, ya dubi gidan ya ce, "Mai gidan nan yau kwananka ya kare, Allah ya kai mu dare." Ya koma gun 'yan uwansa.

Da Murjanatu ta fito daga gida, bayan tafiyar shugaban barayi, ta tsaya ta duba jikin gidansu da kyau ko za ta ga wata sabuwar alama, amma ba ta gani ba. Ta ce a ranta, "Wata kila mai yi musu lamba a jikin gida ya gaji ya watsar, ko wane ne? Oho! Wata kila ma yara ne." Ta kama harakokin gabanta, ba ta koma kan batun ba.

Za mu ci gaba....

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 4

Bayan kwana biyu, barayi suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!"

Ya ci gaba da cewa, "Ina so daya daga cikinku ya yi shiri irin na fatake, ya shiga cikin birni ya shako mana labari daga mutane, wata kila zai ji ana labarin wani mutum da aka kashe ta hanyar daddatsa jikinsa, ta haka za mu gane wanda ya zo nan ya dauke shi, kuma ya ke dibar mana dukiya."

Sai wani barawo daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma na yi alkawrin ba zan komo nan ba sai da cikakken labarin wannan mutum."
Babbansu ya ce, "Wannan aiki ne mai muhimmanci a wurinmu gaba daya, saboda haka idan har ka yi kuskuren da ka dawo nan ba tare da ka gano mana gidan wannan mutumin ba, to zan kashe ka."

Barawo ya ce ya yarda.

Ya yi shiri irin na matafiya, idan ka gan shi kamar wani mutumin kirki. Ya nufi birni. Ya iso cikin garin da sassafe. Da shigarsa cikin gari, sai ya hango wani mutum ya yi sammakon bude rumfarsa yana zaune a ciki. Da ya isa inda wannan mutumin ya ke, sai ya ga ashe dattijo ne, yana zaune yana dinkin takalmi. Ya yi mamakin wannan dattijo da yadda ya yi sammakon bude rumfarsa, bayan duk sauran rumfuna suna a rufe.

Barawo ya yi wa dattijo sallama. Bayan ya zauna sun gama gaisawa sai ya ce masa, "Baba, amma Allah ya hore maka kaifin ido, ta yaya kake iya gani cikin duhun safiyar nan har kake dinki, ga shi kuma ka tsufa?"

Dattijo ya ce, "Ga alama dai kai bako ne a wannan gari namu, idan ba haka ba waye bai sanni ba da kuma lakanin da ake yi mini na 'Baba Mustafa, dila mai idon zinari' ba. Tun ina dan shekara takwas na koyi wannan sana'a ta dinki daga mahaifina, kuma tun lokacin ita nake yi. Kai bari ma ka ji, saboda gwanancewata a dinki, har gawar mutum na taba hadawa na dinke ta wuri daya, bayan da barayi suka yi mata gunduwa-gunduwa, kuma a cikin daki mai duhu na yi wannan aiki."

Barawo ya bude baki cikin mamaki, ya ce a ransa, ga dukkan alamu na taki sa'a a kan wannan bincike da na fito yi, lalle ta hanyar dattijon nan zan sami abin da na fito nema. Ya dubi Baba Mustafa cikin mamaki ya ce, "Ka taba dinke gawar mutum fa ka ce? Kuma a cikin daki mai duhu? Wannan basira taka da yawa ta ke. Amma dai tun kana dan saurayinka ka yi wannan aiki ko?"

Baba Mustafa ya yi dariya ya ce, "Ba a yi kwana hudu da na yi wannan aiki ba. Wata rana ne, da sassafe kamar yanzu, wata yarinya.... Af! Na manta an rantsar da ni a kan cewa kada na yi wannan zance da kowa."

Da jin haka, sai barawo ya jawo jakarsa, ya bude ta sosai ta yadda Baba Mustafa zai iya ganin kudin da ke ciki. Ya lura da yadda Baba Mustafa ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya ga kudin da ke makare a cikin jakar. Ya debo kudin ya ba shi, ya ce masa, "Karbi wannan ka fitar da kono a kan rantsuwar da ka yi, ina so ka fada mini wannan labari, kuma ka kai ni gidan da ka yi wannan aiki. Idan ka yi mini wannan, hakika zan biya ka da kudi mai yawan gaske."

Baba Mustafa ya ce, "Idan dai za ka biya ni ai sai na fada maka labarin duka." Barawo ya debo kudi mai yawa ya ba Baba Mustafa. Shi kuma ya fede masa biri har wutsiya.

Barawo ya ce, "Tashi mu je maza ka kai ni gidan, kafin mutane su fara fitowa zuwa wurin harkokinsu."

Baba Mustafa ya ce, "Ba ka ji labarin dai dai ba ne? Ai yarinyar rufe mini ido ta yi lokacin da za ta kai ni gidan, ba ta bude mini ido ba sai da muka shiga cikin dakin da gawar ta ke. Kuma ina gama aikin ta sake rufe mini ido, sai da muka zo nan sannan ta bude. Ba zan iya gane gidan ba, ko kalar fentinsa ban samu damar gani ba ballantana na ce zan iya shaida shi."

Barawo ya ce, "Ka yi amfani da hikimarka da basirarka mana, ni ma in rufe maka ido ka rika misalta hanyar da kuka bi a cikin zuciyarka har mu isa gidan. Ina tsammanin za ka iya yin wannan."

Baba Mustafa ya ce, "Kwarai kuwa zan iya, domin duk kwanar da muka bi zan iya kiyasta ta a cikin zuciyata. Kai bari ma ta wannan, har takun da muka yi kafin mu isa gidan da kuma bayan mun dawo na lissafe su kaf. Ba fa banza ake yi mini lakabi da dila ba yaro."

Suka tashi, barawo ya sami wani kyalle ya rufe idon Baba Mustafa. Suka shiga cikin gari. Bayan sun dan taba tafiya ta wani lokaci, sai suka iso gaban wani gida. Baba Mustafa ya tsaya, ya ce da barawon nan, "A dai dai nan ne na ji yarinyar nan ta bude kofar gida muka shiga daga ciki."

Barawo ya bude wa Baba Mustafa fuskarsa, ya ce, "Ka tabbata wannan gidan ne?" Baba Mustafa ya tabbatar masa da cewa ko shakka babu.

Barawo ya dubi gidan nan da kyau, da kalar fentinsa. Ga mamakinsa sai ya ga ai kusan duka gidajen unguwar kalar gininsu guda, kuma duk fentinsu kala guda ne. Sai lamarin ya daure masa kai, ya ga cewa idan ya koma ya fada wa 'yan uwansa ya gane gidan, idan suka zo cikin dare ba zai iya shaida gidan har ya nuna shi ba. Don haka sai ya bude jakarsa ya dauko wani bakin fenti da yayi amfani da shi wajen canja kamannunsa, ya zana wata 'yar alama a jikin kofar gidan, yadda idan suka dawo cikin dare zai gane gidan. Ya sallami Baba Mustafa ya koma rumfarsa. Shi kuma ya juya zuwa cikin daji wurin 'yan uwansa domin ya shaida musu cewa bukata ta biya.

Za mu ci gaba....

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 1

Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa. Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan Amina (SAW).

A wani shudadden zamani, a wani gari na cikin kasar Farisa, an yi wadan su mazaje guda biyu yan uwan juna. Babban sunansa Kasim karamin kuwa sunansa Ali Baba. Bayan rasuwar mahaifinsu, aka raba musu gadon yar dukiyar da ya bari, kowa ya kwashi rabonsa.

Kasim ya auri yar wani babban attajiri na garin, shi kuwa Ali Baba ya auri wata yarinya wacce iyayenta sun kasance talakawa ne. Ba a dade ba, sai surukin Kasim ya mutu, yarsa ta gaji dukkan dukiyarsa, domin ita kadai ce yar da ke gare shi. Ita kuma ta damka dukiyar nan a hannun mijinta Kasim. Nan take Kasim ya zama babban attajirin da babu kamar sa a duk fadin garin.

Shi kuwa Ali Baba sai ya kasance dan abin da ya gada na dukiya daga mahaifinsu ya kare. Ya zama talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku. Sai ya rika zuwa daji da jakansa yana saran itace yana lafto wa jakan nan yana kawowa cikin gari. Idan ya sayar, ya siyo abincin da za su ci, shi da matarsa.

Ana nan haka kullum, wata rana Ali Baba ya shiga daji domin yin sana'arsa kamar yadda ya saba. Bayan ya gama dora wa jakansa itace, yana haramar ya kora su ya tafi, sai ya hango 'kura ta toshe sararin samaniya daga nesa, ta tinkaro inda ya ke. Ya ga cewa idan ya ci gaba da tafiya mahayan nan za su cim masa, sai ya kora jakansa cikin rami, shi kuwa ya sami wata babbar itaciya mai duhuwa, wacce zai iya ganin abin da ya ke kasa ba tare da wanda ke kasa ya gan shi ba, ya haye.

Bai jima da hawa saman itaciyar nan ba, sai ya hango mutane akan dawaki a sukwane sun nufo inda ya ke. Suna zuwa wurin, sai duk suka ja suka tsaya. Kowane daga cikinsu ya sauka daga kan dokinsa, ya daure shi. Ali Baba ya dube su da kyau, ya ga cewa dukkansu samari ne majiya karfi, kowane yana rataye da takobi, yana dauke da kaya a kan dokinsa. Ya kirga su, ya ga cewa su arba'in ne cif.

Ashe mutanen nan barayi ne, masu tare fatake suna yi musu fashi, yanzu ma sun zo ne wurin da suke boye kayan da suke satowa. Ali Baba ya ga daya daga cikinsu, wanda yana zaton shi ne babbansu, ya tafi gindin wani dutse da ciyawa ta lullube shi, wanda idan ba yanzu ba Ali Baba bai taba lura da akwai dutse wurin ba. Ya tsaya gaban dutsen ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Dutse ya tsaga gida biyu, sai ga kofa ta bayyana. Barayin nan suka yi ta duruwa ciki da kayan da suka sato, bayan kowa ya shige, sai babban ya bi daga baya. Yana shigewa, sai dutsen ya koma ya rufe, tamkar babu dutse a wurin.

Ali Baba yana kan bishiya, yana kallon dukkan abin da ke faruwa. Bayan barayin nan sun shige cikin dutse, sai yayi kamar ya sauko ya kama doki daya ya hau, ya kora jakansa ya tsere, sai kuma ya tuna idan ya sauko kuma aka yi rashin sa'a da barayin nan suna fitowa daga dutsen nan, lalle za su kama shi. Saboda haka sai ya canza shawara, ya ci gaba da zama a kan bishiyar.

Can zuwa wani lokaci sai ya ga kofar dutsen nan ta bude, shugaban barayin ya fara fitowa ya tsaya a gaban kofar yana kidaya barayin nan a lokacin da suke fitowa, har ya kidaya talatin da tara, gami da shi arba'in ke nan. Da suka gama fitowa, sai Ali Baba ya ji ya ce, "Garam, rufe dutsen Simsim." dutse ya koma ya rufe. Suka hau dawakinsu suka juya ta hanyar da suka fito.

Da Ali Baba ya ga kurarsu ta bace, ya sauko daga kan itaciya, ya nufi inda ya boye jakansa da sauri domin ya kora su zuwa gida, sai wata zuciya ta ce masa, "Ka gwada fadin kalmomin nan ka ga ko dutsen nan zai bude." Ya tafi gaban dutsen ya tsaya dai dai inda ya ga shugaban barayin nan ya tsaya, ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Yana fadar haka kuwa sai kofa ta bude.

Ali Baba ya kutsa kai cikin dutsen nan. Yana shiga sai dutse ya koma ya rufe. Da farko yayi zaton zai ga duhu dindim a ciki, amma sai ya ga haske kamar an kunna fitilu. Ya duba haka, sai ya ga dukiya tsibi-tsibi. Tsibin zinariya daban, tsibin azurfa daban, na tagulla daban, gefe kuma ga kudi nan tsaba cunkus. Ali Baba yayi mamakin yadda wadan nan barayi suka tara dukiya mai yawa haka. Ya ce a ransa, lalle sun gaji dutsen nan ne tun daga kaka da kakanni, domin yawan su ba su isa su tara wannan dukiya ba koda kuwa sun yi shekara dari suna tara ta.

Ya tattaro wasu buhuhuwan zinariya, wadan da ya san jakansa za su iya dauka. Ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Dutse ya bude ya fito da buhuhuwan waje, sannan ya ce, "Garam, rufe dutsen Simsim." Dutse ya koma ya rufe. Ya jawo jakansa ya dora musu dukiyar nan sannan ya dora musu itace daga sama ya rufe yadda mutane ba za su gane ba. Ya kora su da sauri ya nufi gida yana murna.

Da ya isa gida, ya kora jakunan ciki ya kira matarasa suka sauke kayan. Koda ya zazzage, sai wurin ya haske, matar ta ga zinariya tana daukar ido. Ya shaida mata dukkan abin da ya faru. Ta yi godiya ga Allah, ta ce, "Dare daya Allah kan yi bature, hakika duk fadin garin nan yanzu babu wanda ya kai mu arziki. Bari na kidaya na gani"

Ali Baba ya yi dariya ya ce, "Mene ne na batan lokacinki wajen kidaya wannan zinariya? Sai ki yi kwanki ba ki gama gidaya ta ba. Abin da na ke so da ke shi ne, bakinki kanen kafarki, kada ki kuskura wani ya ji wannan labari. Zan je na haka rami mu binne wannan dukiya da Allah ya ba mu."

Matar ta ce, "Duk da haka dai ina so na san adadin wannan zinariya. Kafin ka gama haka rami bari na je nan makwabtanmu, gidan yayanka Kasim na aro karamin mudunsu na awon hatsi domin na ga ko mudu nawa wannan zinariya za ta yi."

Ya ce ba laifi amma ta tabbatar ba ta fadawa kowa abin da za ta auna da mudun ba. Ta fito ta shiga gidan Kasim, ta taras da matarsa. Bayan sun gaisa ta ce ta zo ne aron mudunsu na awon hatsi. Matar Kasim ta tambaye ta babba ko karami? Ta ce karamin ma zai yi. Ta shiga cikin daki domin ta dauko ma ta, ta ce a ranta, me wadan nan matsiyatan za su yi da mudu? Ina kuma suka sami hatsi mai yawa haka da har sai sun auna shi da mudu? Kuma wane irin hatsi ne wannan? Sai ta sami karo kadan ta manna shi a cikin kusurwar mudun wanda ta tabbata karon zai like kwaya daya ta hatsin da za a auna, ta haka za ta iya gano kalar hatsin da suka auna idan an maido mata da mudun. Ta kawo wa matar Ali Baba.

Bayan ta dawo gida, sai ta fara auna zinariyar nan mudu-mudu har ta gama kaf. Ta je ta sahida wa mijinta da yake hakar rami ko mudu nawa ta auna. Ta ce za ta je ta mayar musu da mudunsu. Ashe ba ta lura ba, kwayar zinariya daya ta manne da karon nan a can kasan mudun. Da matar Kasim ta karbi mudu, bayan matar Ali Baba ta tafi, sai ta duba cikin mudun. Wani irin mamaki ya rufe ta lokacin da ta ga kwayar zinariya a cikin mudun.

Nan take hassada ta daki kirjinta ta ce, ashe Ali Baba har yana da zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai awo da mudu. Ina ya sami wannan dukiya? Ko ya fara sata ne? Bari mijina ya dawo in fada masa halin da kanensa yake ciki.

Za mu ci gaba....

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 2

Lokacin da Kasim ya dawo daga kasuwa tun bai huta ba, matarsa ta tare shi ta ce, "Maigida, na san da cewa ka dauki kanka a matsayin wanda ya fi kowa arziki a duk fadin garin nan, to amma abin da ba ka sani ba shi ne, yanzu akwai wanda ya dame ka ya shanye game da arziki cikin wannan gari namu. Domin yana da tarin zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai a auna ta da mudu."

Kasim ya ce, "Wane ne wannan attajiri haka, amma dai bai dade da zuwa garin nan ba ko?"

Matar ta ce, "Ba kowa ba ne face dan uwanka Ali Baba." Ta kwashe dukkan labarin yadda matar Ali Baba ta zo aron mudu a wurinta, da kuma dabarar da ta yi har ta gano abin da aka auna da mudun.

Kasim ya kasance ba ya kula da taimakon dan uwansa Ali Baba duk da tarin dukiyarsa, ba ya ko yarda ya matso kusa gare shi, wai kada ya shafa masa talauci. Da ya ji wannan labari daga matarsa, sai ya cika da mamaki tare kuma da hassadar jin cewa wai har akwai wanda ya fi shi arziki a garinsu. Ya ce a cikin ransa, "Yanzu dare ya yi, amma gobe tunda safe zan je gidan dan uwana na ji inda ya sami wannan dukiya da rana tsaka. Lalle idan ya fara sata ne, zan tsegunta wa Sarki a daure shi." Ya kwanta amma ya kasa yin barci, yana ta kahon dandi har gari ya waye.

Da gari ya waye, tunda sassafe Kasim ya sallama wa Ali Baba. Bayan ya fito, ko gaisawa ba su yi ba, sai Kasim ya ce, "Ali Baba ka yi wa mutane badda sau, suna ganin ka a matsayin talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku da kake zuwa daji kana yiwo itacen siyarwa. Amma abin mamaki, jiya bayan na dawo daga shagona, matata ta ba ni wannan kwayar zinariyar ta ce mini a cikin mudun da ta ara muku ta makale. Wannan ya tabbatar mata da cewa ba hatsi kuka auna da mudun ba. Wannan ne dalilin da ya sa yanzu na yo maka sammako domin na ji inda ka sami wannan dukiya, idan kuwa ka ki fada mini zan je na shaida wa Sarki cewa kana daya daga cikin barayin nan da suka addabi mutanen wannan gari da kewayensa da sata, yanzu haka ma zinariya na nan kime a gidanka da kuka sato. Kuma na tabbata idan aka bincike gidanka kaf, za a gan ta."

Da Ali Baba ya ji wannan zance na dan uwansa, sai ya tabbatar da cewa matarsa ta fallasa musu sirrinsu ba tare da ta sani ba, don haka babu wani boye-boye illa ya fada wa dan uwansa gaskiyar abin da ya faru.

Ali Baba ya kwashe labrin abinda ya faru duka ya fada wa Kasim. Ya yi masa kwatancen dajin nan da kuma dai dai wurin da dutsen da barayin nan suke tara dukiyarsu ya ke. Ya kuma fada masa abin da ake cewa dutsen ya bude da kuma abin da ake cewa ya rufe.

Kasim na gama jin wannan labari, bai zame ko'ina ba sai kasuwa. Ya siyo jakai guda goma, kowane da mangalarsa, ya kawo gida ya daure.

Tun da asuba ya daura wa jakuna mangaloli, ya nufi dajin nan da Ali Baba ya yi masa kwatance. Can zuwa rana tsaka ya isa, ya bi kwatancen da aka yi masa har ya gano wurin da dutsen ya ke. Ya daure dabbobinsa a kusa da dutsen.

Ya tsaya gindin dutse ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Rufe bakinsa ke da wuya, sai ya ga kofa ta bude daga jikin dutsen. Mamaki ya rufe shi, nan da nan ya kwanto mangaloli daga jakunansa ya kutsa kai cikin dutsen, yana shiga dutsen ya rufe.

Kasim ya ga ashe dutsen wani katon daki ne mai cin dakuna sama da uku. Ya ga tarin dukiyar da ko a tunani bai taba zaton akwai irinta ba a fadin duniya. Komai bangarensa dabam, zinariya da azurfa da tagulla da tsabar kudi, ga su nan bila haddin. Ba tare da bata lokaci ba, ya fara cika mangalolinsa da ita yana tunanin abubuwan da zai yi idan ya kwashe ta duka ya kai gida.

Da ya gama cika mangalolinsa, ya ga kamar ma bai debi komai ba, domin babu alamun dukiyar nan ta ragu. Ya kiyasta cewa koda zai kwashe dukiyan nan duka, to sai ya yi wata uku ko fiye yana zuwa kullum yana dibar ta. Ya zo inda kofar dutsen ta ke ya ce, "Fayau, bude dutsen Cimcim." dutse ya ki budewa. Ya kara cewa, "Fayau, bude dutsen Jimjim." Dutse bai ko motsa ba.

Kasim yayi ta kiran kalmomi kamar su, Timtim, Kimkim, Zimzim, amma Allah da ikonsa har ya gaji ya kasa tuna kalmar "Simsim." Kamar ma da dai, bai taba jin kalmar ba. Daga nan sai murna ta koma ciki, domin ya tabbata idan barayin nan suka dawo suka same shi a ciki, lalle kashinsa ya bushe.

Sai duk dukiyar da ke cikin dutsen ta fita daga ransa, ya fara safa da marwa yana kokarin tuna kalmar da ake fada dutsen ya bude. Yayi duk iyakar kokarinsa amma ya kasa tuna kalmar. Da ya gaji sai ya sami wuri ya zauna yana tunanin makomarsa idan barayin nan suka same shi a cikin ma'ajiyarsu.

Bai san tsawon lokacin da ya kwashe a cikin dutsen ba. Can sai ya ji karar kofatan dawaki suna nufo wurin da dutsen ya ke. Tun yana jiyo su daga nesa, har suka zo daf da gindin dutsen. Daga nan sai ya ji duk sun sauka daga kan dawakansu. Ya duba cikin dutsen nan ko zai ga wani makami da zai kare kansa da shi, bai samu ba. Ya duba ko akwai wani wuri da zai iya boyewa, ya ga babu. Ya yanke shawarar ya tsaya daf da bakin kofa, idan dutsen ya bude sai ya yi wuf ya yi waje da gudu ya kama dokinsu daya ya sukwane shi, idan Allah ya taimake shi zai iya tserewa. Don haka sai ya tsaya daf da wurin da kofar za ta bude cikin shiri.

Su kuwa barayin nan da suka zo gindin dutse sai suka ga jakai guda goma a daure, suka duba ko'ina ba su ga mai su ba. Sai jikinsu ya ba su, domin ba su taba sa ran wani dan Adam zai iya zuwa cikin wannan daji ba, kuma har gindin dutsensu. Babbansu ya matsa gaban dutsen ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Nan take dutse ya bude.

Za mu ci gaba....

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 3

Kofa na budewa, sai Kasim ya fito waje da gudu, ya bangaje wasu daga cikin barayin nan. Kafin ya sake daga kafarsa wani daga cikin barayin nan ya raba shi gida biyu da takobinsa, gaya-wa-jini-na-wuce.

Barayin nan suka shiga cikin dutsen, suka ga mangalolin da Kasim ya cika da dukiyarsu. Kuma suka lura da cewa lalle ko bayan wannan dukiyar da Kasim ya dauka, akwai alamun an taba dibar dukiyar, ke nan ko Kasim din ne ya taba diba yanzu ya dawo ya kara, ko kuwa akwai wani bayan Kasim din wanda ya dibar musu dukiya.

Suka yi mamakin yadda Kasim ya san kalmomin da ake fada dutsen ya bude. Domin su gargadi duk wani mai zuwa yana dibar musu dukiya, sai suka raba gangar jikin Kasim gida hudu, suka manna kowanne sashe daya a bango daya na dutsen, watau kudu da arewa, gabas da yamma. Suka fita suka kora jakunansa zuwa inda suke tara dabbobin da suke satowa.

Da dare ya yi matar Kasim ba ta ga ya komo gida ba, sai hankalinta ya fara tashi. Ta dauki mayafinta ta ruga da gudu zuwa gidan Ali Baba. Ta same shi yana zaune yana hutawa.

Bayan sun gaisa, sai ta ce masa, "Ya kai dan uwan mijina, na san cewa kana da labarin mijina ya shiga daji da jakai, tunda assalatu, akan zai samo wani abu a can, wanda bai fada mini ko mene ne ba. Ga shi har dare ya yi bai komo ba. Shi ne na zo gare ka na ji ko ka san wurin da ya tafi? Ina jin tsoro, ya Allah ko wani mummunan abu ya faru da shi"

Ali Baba ya ce da ita, "Haka ne, dan uwana ya fada mini zai shiga daji, ai na dauka ya dawo, amma bari yanzu na shirya na tafi neman labarinsa. Ki koma gida zan sanar da ke abin da ake ciki idan na dawo."

Ali Baba ya tashi cikin daren nan ya daura wa jakansa uku mangaloli, ya kora su ya nufi cikin dajin da dutsen 'yan fashin nan ya ke. Can zuwa tsakiyar dare ya isa inda dutsen sihirin ya ke. Da isarsa gindin dutsen ya haska fitilarsa, sai ya ga jini faca-faca ko'ina a gindin dutsen. Tun daga nan sai ya sha jinin jikinsa. Ya ce, "Fayau bude dutsen simsim." Nan take kofa ta bude, ya shiga ciki.

Da shigarsa sai kofa ta rufe, ya haska fitilarsa, sai ya ga gawar dan uwansa Kasim, an datsa ta gida hudu, an manna kowane datse a bangon dutsen. Nan take ya yi sauri ya harhada su wuri daya. Sannan ya kuma dibar dukiyar da jakansa biyu za su iya dauka, ya fita daga cikin dutsen. Ya dora wa jakinsa daya gawar dan uwansa, sauran biyun kuma ya dora musu dukiyar da ya diba, ya samu kiraren itatuwa ya rurrufe mangalolin da su, yadda mutane ba za su gane abin da aka dauko ba. Ya kora su da sauri ya nufi gida.

Can zuwa da hantsi Ali Baba ya isa gida, ya shiga da jakansa biyu masu dauke da dukiyar cikin gida, ya fada wa matarsa ta sauke kayan ta boye su inda suka boye na farko. Ya kora jakin daya zuwa gidan matar dan uwansa.

Da ya isa gidan sai ya kwankwasa kofa. Bayan kwankwasawa ta biyu, sai ya ga Murjanatu ta bude kofar. Murjanatu ta kasance baiwa ce ga Kasim, Allah ya hore ma ta tsananin wayo da dabara, duk da ta kasance yarinya karama, mai kananan shekaru, amma hankalinta da tunaninta ya zarta na manyan mutane. Shi ya sa ma duk wata shawara da ita Kasim ya ke yi.

Ali Baba ya kora jakinsa cikin gidan, Murjanatu ta mayar da kofa ta rufe, ya umurce ta da ta kira masa matar dan uwansa. Bayan sun koma, ya sauke gawar Kasim ya shaida musu abin da ya faru da Kasim duka. Bayan sun gama yan koke-kokensu, sun share hawaye, sai ya ce musu, "Abin da na ke so da ku shi ne, ina so mutanen garin nan su tabbatar da cewa dan uwana ya mutu ne a gida, a kan gadonsa, sanadiyyar rashin lafiya, ba na so kowa ya san abin da ya faru da shi."

Abin da ya sa Ali Baba ya fadi haka kuwa shi ne, ya tabbata idan barayin nan suka koma maboyarsu ba su ga gawar Kasim ba, za su shiga binciken wanda ya zo ya dauke ta. To idan mutanen gari suka san gaskiyar labarin yadda Kasim ya mutu, da yadda aka rufe gawarsa guntu-guntu, labarin ba zai boyu ga barayin nan ba, kuma za su yi saurin gane Ali Baba su kashe shi. Amma idan mutanen gari suka san cewa Kasim ya mutu ne a kan gadonsa sanadiyyar rashin lafiya, kuma an yi jana'izarsa gaban mutane, shi ke nan babu wanda zai koma ta kan batun. Don haka babu yadda za a yi barayin su gane wanda ya dauke gawar.

Bayan Ali Baba ya tafi, sai matar Kasim ta ce da Murjanatu, "Na bar wannan a hannunki, ke kika san dabarar da za ki yi, ki kawar da hankalin mutane har su dauka cewa Kasim ya mutu ne sanadiyyar rashin lafiya a kan gadonsa."

Murjanatu ta ce, "Wannan abu ne mai sauki a wurina." Sai ta ruga da gudu zuwa shagon wani mai sayar da magunguna, hankalinta a tashe, ko takalmi babu a kafarta, ta ce da shi, "Don Allah yi sauri ka bani maganin zazzabi, ubangijina Kasim na can zazzabi mai zafi ya rufe shi, har ba ya iya gane masu zuwa wurinsa."

Mai magani ya dauko wani magni ya ba ta. Ta karba ta ba shi dirhami daya, ba ta ko tsaya karbar canji ba, ta nufi gida da sauri, ta na rike da magani a hannunta, tana tafe hawaye na fita daga idonta. Duk wanda ta hadu da shi a kan hanya, idan ya ga halin da take ciki, ga kuma magani a hannunta, sai ya tausaya mata, ya kuma gane abin da take ciki na jiyyar mara lafiya.

Ali Baba da matarsa suka dinga Safa da Marwa tsakanin gidansu da gidan Kasim, domin dai su baddalar da mutane a kan cewa wani abu na faruwa a gidan Kasim. Don haka lokacin da mutane suka ji kuka daga gidan Kasim tare kuma da labarin mutuwarsa cikin dare ba su yi mamakin hakan ba.

Tun da sassafe kafin Ali Baba ya gama shaida wa mutane labarin mutuwar dan uwansa Kasim, domin yi masa jana'iza, ita kuwa Murjanatu sai ta nufi shagon wani baduku, dattijo mai suna Baba Mustafa, domin dama dabi'arsa ce da an fito daga sallar subahi yake bude shagonsa.

Ta same shi a zaune cikin shagon, bayan ta yi masa sallama sun gaisa, sai ta ce da shi, "Baba Mustafa ina da wani aiki da nake so ka yi mini yanzu, amma da sharadi daya." Ta dauko dinari daya ta danka masa a hannu.

Ya yi sauri ya karbe yana murmushi, dama idonsa idon kudi kamar wuta da auduga ne, ya ce da ita, "Diyata, fadi abin da kike so na yi miki, ko menene idan dai zan iya yin sa, to zan yi miki shi duk da dai ban san ki ba, ban ma taba ganin ki ba."

Murjanatu ta ce da shi, "Jiya cikin dare barayi suka shiga gidanmu suka kashe mijina kuma suka sassara shi guntu-guntu. Ina so, a matsayinka na baduku, ka harhada gawarsa wuri daya ka dinke, yadda za a ji dadin yi masa jana'iza. Amma da sharadin zan rufe fuskarka da mayafi ta yadda ba za ka iya gane hanyar da muka bi zuwa gidan ba, kuma ba za ka iya gane gidan ba. Haka kuma idan ka gama zan sake rufe fuskarka na maido ka shagonka. Zan biya ka kudi mai yawa, ka yarda da wannan sharadi?"

Baba Mustafa ya ce ya amince. Murjanatu ta rufe masa fuska, ta ja hannunsa har suka isa gidan, ta bude kofa suka shiga ciki, ta ja shi har cikin dakin da gawar Kasim ta ke, sannan ta bude masa ido. Ta ce ya yi sauri ya hada shi masu jana'iza na nan zuwa. Nan take kuwa ba tare da bata lokaci ba Baba Mustafa ya dinke gawar Kasim wuri daya, kamar ba a taba sassara ta ba. Murjanatu ta ba shi kudi masu yawa, sannan ta rufe masa idanu ta mayar da shi shagonsa.

Aka yi jana'izar Kasim aka gama ba tare da kowa ya san gaskiyar abin da ya faru gare shi ba.

Su kuma barayin nan bayan kwana biyu suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!"

za mu ci gaba....

DARE DUBU DA DAYA

CIKAKKEN BAYANI GAME DA RIJISTAR SHIGA ZAUREN DARE DUBU DA DAYA NA FACEBOOK.

Amincin Allah ya tabbata a gare ku.

Ganin yadda jama'a suke ta nuna sha'awarsu game da hikayoyin wannan littafi na Alfu Laila wa Lailah ko kuma DARE DUBU DA DAYA, shi ya sa ni (Bukar Mada), da Professor Ibrahim Malumfashi, da wani marubuci mai suna Danladi Haruna, muka yanke shawarar samar da cikakken wannan littafi (tun daga dare na 1 har zuwa Dare na 1001) da Hausa domin al'ummar Hausawa su sami abin karantawa.

Littafin DARE DUBU DA DAYA shahararen littafi ne na Larabawa da ya yi fice a fadin duniya gaba daya. An fassara shi cikin harsunan duniya da yawa, ciki har da Hausa. Na hausar an fassara shi fiye da shekara dari (100) da suka wuce, lokacin babu Typewriter ko computer a kasar Hausa, wani bature ne mai suna Frank Edgar ya rubuta tare da taimakon wasu Malamai na kasar Sokoto, don haka da hannu aka yi rubutun (kamar yadda kuka ga samfur din rubutun a cikin wannan hoto).


Rubutun na nan a cikin taskar ajiyar tsofaffin bayanai na Kaduna, fayil goma sha hudu (14). Kowane fayil akwai takarda 700 zuwa 800 ciki. Shi ne Kamfanin NNPC suka buga littafi biyar daga fayil na farko (duk littafi daya na NNPC ana sayar da shi N500 ne a kasuwa, idan kuka hada littafi biyar, watau fayil guda kenan, kudinsu ya kama N2,500). Sauran fayilolin ba a kuma kula su ba, balle a buga su, su zama littattafai.

Ganin irin muhimmancin aikin a Adabin duniya shi ne muke wannan yunkurin yanzu na ganin mun juya wannan rubutun hannu, na dukkan fayilolin 14, zuwa rubutun computer, sannan mu buga littattafan don sayarwa ga al'umma. Hoto (photocopy) kawai na takardun da muka yi, sun lashe kudi sama da dubu saba'in (N70,000). Kenan wannan ba karamin aiki ba ne, sai an nemi gudummawa ga jama'a.

Daga nan sai muka yanke shawarar kirkirar wani zaure (Goup) a FACEBOOK, wanda duk rubutun da muka juya na wadancan takardun, za mu rika tura (posting) su a cikin zauren har zuwa lokacin da muka gama juya su gaba daya. Mun kiyasta aikin zai kai mu shekara daya da 'yan watanni. Duk wanda yake da sha'awar shiga wancan zauren zai ajiye kudin rijista, wanda da kudin ne za mu rage wasu ayyuka na buga littafin.

A baya, mun kasa rijistar kamar haka:

Wata daya a cikin zauren N1,000

Wata biyu N2,000

Wata uku N2,500 (amma a jere)

Wata shida N5,000 (shi ma a jere)

Shekara daya N10,000

Sa'annan idan an kammala aikin littafin, wadanda suka yi rijista su ne za su fara samun littafin da rangwamen farashi gwargwadon rijistar kowa. Idan ta N1,000 aka yi za a sami ragin 10%, ta N2,000 kuma 20%, ta N5,000 kuma 50%. Idan aka yi ta shekara watau N10,000 za a sami ragin 100%, watau za a sami duka littattafan kyauta.

To, amma yanzu ga yadda sabon tsarin yake:

Bisa la'akari da koke-koke da kuma korafin mutane da dama, sannan kuma da la'akari da halin rashi da mafi yawancin 'yan kasar nan suke ciki, mun yanke shawarar mayar da rijistar shiga ZAURUKAN sau daya har zuwa lokacin gama karatun littafin gaba daya. Dangane da haka ga sababbin tsare-tsaren shiga ZAURUKAN DARE DUBU DA DAYA da aka amince da su.

1. Duk wanda zai shiga ZAURUKAN zai biya kudin rijista ta Naira DUBU DAYA (N1000) ne kacal har a gama karanta duka littafin.

2. Wannan kudin rijista na N1,000 na karatu ne kawai a facebook, bai shafi mallakar kwafin littattafan ba idan sun fita kasuwa.

3. Idan ana bukatar kwafin littattafan, to, tsohon tsarin rijista yana nan. Watau za a biya Naira dubu goma (N10,000), kuma za a ci gaba da biya sannu a hankali har a ajiye kudin kafin kammala aikin littattafan.

4. Idan kuma an fara biyan kudin kwafin littattafan sai wata matsala ta sa mutum bai cika kudinsa ba, to, zai sami rangwame gwargwadon kudin da ya ajiye (idan ya ajiye 2,000 ne zai sami rangwamen 20%. Idan 5,000 ne zai sami rangwamen 50%) kamar dai yadda tsohon tsarin yake.

5. Duk wadanda suka rigaya suka yi rijista ta tsohon tsari, watau watan Disamba da Janairu, to, za a cire Naira dubu 1,000 a matsayin kudin rijista na gaba dayan shekarar, abin da ya yi saura na daga kudinsu, sun zama zubi a kan mallakar kwafin littattafan idan an gama aikinsu.

Misali:

(I). Wanda ya yi rijista ta wata daya, N1000 ya biya kudin rejista kenan baki daya har a gama karatun littattafan. Idan yana bukatar kwafin littattafan kuma zai iya ci gaba da zuba kudin har ya tunfaye sauran N9,000. Idan kuma bai da bukatar mallakar kwafin, to, shi ke nan.

(II). Wanda ya biya kudin rijistar wata uku, N2500, za a cire N1000 na sabon tsarin rijista, sauran kudi, N1500 sun zama zubi. Zai iyar da cika N8,500 domin mallakar kwafi, idan kuma bai da dama, har aka gama aikin littafin bai cika ba, to, zai sami ragi na 20%.

(III). Wanda ya yi rijistar wata shida, N5,000, za a cire N1000 na sabon tsarin rijista, saura N4,000 sun zama zubi na kwafin littafi. Sai ya cika N6000 domin mallakar littafin kyauta. Idan kuma bai sami halin cikawa ba zai sami ragi na 50%.

(IV). Wadanda suka yi rejista ta shekara kuwa, N10,000, to, kwafin littattafan kawai suke jira Idan an kammala karatu da aikin littafin.

6. A halin yanzu, duk wadanda suka rigaya suka yi rijista, kuma suke cikin zauren na DARE DUBU DA DAYA, ba ya da bukatar sabunta rijista, kamar yadda tsohon tsarin ya tanadar, har mu kammala karatu, sai dai a yi kokarin ajiye kudin mallakar kwafin littafin. Zuwa yanzu mun sami mutane da dama da suka yi rijista.

Ko da rijista, ko babu, mu dai mun sha alwashi sai mun juya wannan rubutun hannu zuwa rubutun computer, sannan duk yadda za a yi sai mun samar da cikakken wannan littafi ga al'ummar Hausawa, kamar yadda wasu harsunan duniya suka fassara shi ga al'ummarsu. Idan ba a sami yin rijista ba, to a taimaka mana da addu'a, domin ganin mun iyar da aikin da kakanninmu suka faro tun shekara dari da suka wuce. Sannan sai a jira fitowar littattafan a kasuwa, nan da shekara daya, In Sha Allah.

GA YADDA ZA A BIYA KUDIN RIJISTA:

• Ga wadanda za su biya a banki ga asusun ajiyar da za a tura kudin rejista kamar haka:

* Bankin UNITY:
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 0018960303.

* Bankin UBA:
SUNA: Ibrahim Malumfashi,
Lambar asusu: 2018484292.

Ana kuma iya sayen katin waya na adadin kudin rijistar da za a yi, sai a tura wa wannan lambar 08066699976 (amma katin MTN kawai). Idan za a tura katin sai a hada da sunan da ake amfani da shi a facebook, domin mu san wanda ya turo.

KARIN BAYANI

Idan muka yi la'akari da littattai biyar da NNPC suka buga daga fayil guda, kudinsu ya kama N2,500. To, da za a ce littattafan nan biyar sun zama littafi guda (daga fayil guda) a yi sauran fayilolin sha hudu, to, nawa kudin littattafan gaba daya za su kama idan aka buga dukkan fayilolin gama sha hudu? Kenan za su kama; N2,500 x 14 = N35,000.

To, amma mu, ga shi za mu buga dukkansu a N10,000 kacal. Amma fa wannan garabasar ga wadanda suka yi rijista ne kawai. Wadanda ba su yi ba, za su saye shi daidai farashin da kowa zai saye a kasuwa.

Domin karin bayani kai waye, ko kuma idan an biya kudin rijista, sai a tuntubi daya daga cikin wadannan mutane:

1. Farfesa Ibrahim Malumfashi
Phone: 08035924022
Email: mfashi@yahoo.com
Facebook: http://facebook.com/malumfashii

2. Bukar Mada
Phone: 08021218337
Email: bukarmada@gmail.com
Facebook: http://facebook.com/bukarmada

3. Danladi Haruna
Phone: 08030764060
Email: dharuna@gmail.com
Facebook: http://facebook.com/dharuna

ALLAH YA YI MANA JAGORA.