Thursday 10 July 2014

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 7

Da gari ya waye, Ali Baba ya fito farfajiyar gidan domin su gaisa da bakonsa, ga mamakinsa sai ya ga kofar dakinsa a bude, babu bako babu alamunsa, amma kuma ga dabbobinsa nan da kuma hajarsa ta mai. Yana nan tsaye yana mamakin inda bakonsa ya shiga, sai ga kuyangarsa Murjanatu ta fito, ta durkusa ta gaishe shi.

Ya tambaye ta, ko ta ji motsin bakonsa? Domin tagar dakinta na kallon farfajiyar gidan ne, duk wani motsi da za a yi a farfajiyar gidan Murjanatu za ta iya ji daga cikin dakinta. Ta ce da Ali Baba, "Maigida zo ka duba da idonka, ka kara yi wa Allah godiya, da ya kubutar da kai." Ta ja shi har zuwa wurin da jakunkunan mai suke, ta ce ya bude daya da kansa ya ga abin mamaki.

Ali Baba ya bude jakar mai daya, sai ya ga mutum a ciki, rike da takobi. Ya juya zai gudu cikin tsoro, Murjanatu ta dakatar da shi. Ta ce, "Wannan mutum da kake gani ba zai iya cutar da kai da komai ba domin kuwa ba shi da rai. Mutum talatin da bakwai ne, duk Allah ya ba ni nasarar kashe su da tafasasshen mai." Ta kwashe labarin abin da ya faru duka tun daga lokacin da ta ga ana yi wa gidansu lamba, da kuma yadda ta zo dibar mai a cikin hajar bako, ta gane mutane ne a ciki, da yadda ta kona su da mai, da kuma yadda ta ga shugaban barayi ya bude gida cikin dare ya arce, da ya gano cewa an kashe masa mutane.

Ali Baba ya yi mamaki a kan hikima da kuma dabara ta wannan yarinya, gayar mamaki. Ya gode mata, godiya mai yawa, kuma ya yi mata abishir da wata kyauta mai tsoka, amma bai fada mata ko mene ne ba. Ya tura ta ta kira masa wani bawansa mai suna Abdallah.

Da Abdallah ya zo, Ali Baba ya fada masa abin da ke faruwa. Ya ce yana so su tafi lambun da ya ke cikin gidan su gina katon rami mai fadi da zurfi, wanda zai iya daukar barayin nan duka, su rufe su ciki. Ali Baba ya taimaka wa bawansa Abdallah suka gina katon rami, Allah ya taimake su akwai danshi a cikin lambun, saboda haka ba su sha wata wahala ba wurin haka ramin.

Suka rika ciccibo gawar barayin nan, daya bayan daya, suna jefawa cikin ramin duk da jakunkunan da suke ciki, har suka jefa su duka. Suka mayar da kasa suka rufe. Ali Baba ya gargadi bawan nan, duk da yake ya san amintacce ne, a kan kada ya kuskura ya yi wannan zance da kowa a waje. Jakan barayin nan kuwa, sai Ali Baba ya rika dibar biyu, uku, yana tura Abdallah da su kasuwa yana sayar masa, tunda ba wani amfani zai yi da su ba, har suka kare.

Shugaban barayi kuwa da ya gudu daga gidan Ali Baba, sai ya koma maboyarsu a cikin daji. Ba da jimawa ba, kadaici da kuma tsoro suka lullube shi, ya ji kwata-kwata ba zai iya zama shi kadai a cikin daji ba. Saboda haka sai ya debi wani abu daga cikin dukiyar nan, ya yi shiri kamar wani bakon alhaji, ya koma cikin gari.

Da ya isa cikin gari sai ya tasar wa fada. Aka yi masa iso gun Sarki, ya ce shi bako ne, sunansa Koja Husaini, yana so ya zauna a cikin wannan gari idan Sarki ya yarda, idan ma zai samu gida na siyarwa, to zai siya ya zauna a ciki. Sarki ya sa dillalai suka nemo wa Koja Husaini gida, aka yi ciniki ya biya. Kwamfa! Ashe gidan kuma yana makwaftaka ne da tsohon gidan Ali Baba wanda ya tashi a ciki, ya koma gidan Kasim, wanda kuma yanzu babban dansa ne, saurayi dan kimanin shekaru ashirin da uku, a ciki.

Koja Husaini ya tare cikin sabon gidansa, lokaci-lokaci kuma yakan koma maboyarsu ya debo wani abu daga cikin dukiyarsu, wadda yanzu ta zama mallakarsa shi kadai. Amma ya kan yi taka-tsan-tsan duk lokacin da zai tafi, domin kada ya ja hankalin mutane su fara zarginsa. Kullum zuciyarsa cike take da tunanin hanyar da zai bi ya kashe Ali Baba.

Sannu a hankali Koja Husaini ya fara sabawa da makocinsa, dan Ali Baba, duk da yake ba sa'arsa ba ne, har ta kai ga wani lokaci suna zaunawa su yi ta hira a tsakaninsu.

Ana nan wata rana sai Ali Baba ya kawo wa dansa ziyara a gida, a lokacin kuma Koja Husaini na zaune a kofar gidansa, karkashin wata bishiya, yana hutawa. Da ganinsa, nan take Koja Husaini ya shaida shi. Ali Baba ya shige gidan dansa, bai ko lura da wani mutum ba, ballantana ya lura da ana kallonsa.

Bayan wani lokaci, Ali Baba ya fito daga gidan ya yi tafiyarsa. Ba a dade ba kuma sai ga dansa ya fito, da ya ga Koja Husaini zaune a kofar gidansa, sai ya nufi can domin su yi hira. A cikin hirar tasu ne Koja Husaini ya fahimci cewa wannan yaro, wanda ya zama tamkar abokinsa a halin yanzu, dan Ali Baba ne, babban makiyinsa a duniya. Don haka sai ya raya a zuciyarsa, bari ya ja shi a jika, wata kila ta sanadiyarsa zai cimma burinsa na kashe Ali Baba.

Tun daga wannan rana sai alakar Koja Husaini da Dan Ali Baba ta dauki sabon salo. Koyaushe Koja Husaini ba ya da wani aboki da ya wuce Dan Ali Baba, ya yi ta jan sa a jika har suka shaku da juna suka zama tamkar abokai sa'o'in juna.

Ina ya Allah, babu ya Allah! Ana nan sai matar Ali Baba ta haihu. Tun kafin ranar suna Ali Baba ya shirya wata 'yar gajeruwar liyafa ta cikin gida, watau iyalansa da barorinsa kawai. Da Dan Ali Baba zai je wurin liyafar sai ya gayyaci babban abokinsa, Koja Husaini, domin ya raka shi. Koja Husaini ya yi matukar farin ciki a ransa, damar da yake ta faman jira kwana da kwanaki yanzu ta samu. Idan suka tafi, zai yi iyakar kokarinsa ya kebe da Ali Baba wani wuri, inda babu kowa, ya kashe shi ya gudu, lokacin da duk hankulan iyalansa suke wurin liyafar. Sai ya dauki wata sharbebiyar wuka ya sulle ta a cikin rigarsa, suka tafi.

Ko da suka isa gidan, komai ya kankama. Dan Ali Baba ya gabatar da abokinsa ga mahaifinsa, sannan suka sami wuri suka zauna. Duka-duka wurin liyafar bai wuce mutum biyar zuwa shida ba; Ali Baba da matarsa, Dan Ali Baba da abokinsa Koja Husaini, Abdallah bawan Ali Baba, sai kuma yarinya Murjanatu da take ta faman kawo kayan ciye-ciye da shaye-shaye.

Murjanatu na cikin rarraba abinci ga mahalarta liyafa har ta zo kan Koja Husaini. Tana ganinsa, nan take kwakwalwarta, mai kama da kwamfuta, ta gane shi. Shugaban barayin nan ne ya sake dawowa. Tabbas wannan zuwan ma, akwai manufar da ya zo da ita, ba liyafar ce ta kawo shi ba. Ta kanne abin a cikin ranta, ba ta ce komai ba, ba ta kuma nuna alamun komai ba, tana tunanin hanyar da za ta yi maganin wannan barawo.

Bayan liyafa ta kankama, kowa ya fara motsa bakinsa da abin da aka tanadar. Tuni kuma Murjanatu ta gano wata dabara da za ta kashe wannan barawo. Ta rada wa bawan nan Abdallah, ya dauko dundufarsa ya fara kida ita kuma za ta yi rawa, kamar yadda suke yi wa Ali Baba a duk lokacin da yake bukatar nishadi. Abdalla ya jawo dundufarsa ta kida, ya fara kadawa a hankali, dama kuma gwanin kida ne, ita kuma Murjanatu ta tashi ta fara taka rawa, abin gwanin ban sha'awa.

Al'adar garin ce, idan mace tana rawa a cikin maza, ta kan rike wata 'yar karamar wuka a hannunta. Idan ta yi rawa, ta yi juyi, sai ta zo gaban mutum ta daga wukar nan kamar za ta daka masa ita a zuciya, sai ta juya wukar ta daka masa marikin wukar. Sai a yi tafi, a yi shewa, ta haka ake gane namiji mai tsoro da kuma jarumi. Duk kasar kowa ya san da wannan al'ada, hatta Koja Husaini ya san da haka.

Saboda haka lokacin da Murjanatu za ta fara rawa, sai ta dauko 'yar karamar wuka ta rike a hannunta, tuni ta ayyana abin da za ta yi a cikin ranta. Ta fara rawa tana juyi, ta zo kan mai kida, Abdallah, ta daga wukar kamar za ta daba masa ita, sai ta daba masa kotarta, aka yi tafi. Ta wuce wurin Dan Ali Baba, ta yi kamar yadda ta yi wa Abdallah, ta wuce. Ta je kan Shugaban barayi, ta daga wukar nan, ta tattara iyakar karfinta a hannunta mai wukar ta kirba masa ita a kahon zuciya. Nan take barawo ya fadi kasa yana shure-shure har ya mutu.

Ko da Ali Baba da dansa suka ga wannan danyen aiki da Murjanatu ta aikata, wanda ba su san dalili ba, sai suka taso mata, hankalinsu a tashe, suka far mata da fada, don me za ta kashe bakon da suka gayyato, laifin me ya yi mata. Murjanatu ta dakatar da su, sannan ta bayyana musu ko wane ne wannan bako, sannan ta ce musu, "Duk da yake ban san manufar da ya shigo da ita wannan gida ba, amma na tabbata manufarsa ba ta alheri ce ba."

Da suka duba jikin shugaban barayi, sai suka samu sharbebiyar wuka sulle a cikin rigarsa. Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Murjanatu ta kubutar da rayuwar Ali Baba daga halaka. Saboda haka yanzu ne zai sanar da ita albishirin da ya boye mata a cikin zuciyzrsa, wanda kuma ya taba furta mata.

Ali Baba ya dubi Murjanatu ya ce, "Daga yau na 'yanta ki, kin zama 'ya mai cikakken iko, kuma idan kin yarda ina so ki amince da dana ya zama mijinki." Sannan ya juya wurin dansa ya ce da shi, "Ya kai dana, na san da cewa ba za ka ki amincewa da zabina ba, ka amince na aura maka Murjanatu domin na tabbata ta dace da kai, kuma ba domin ita ba da wannan abokin naka ya sami galaba a kaina, dama ya yi kokarin yin abota da kai ne domin ya samu ya kashe ni. Na tabbata da bukatarsa ta biya, kai ma ba zai bar ka ba. Don haka wannan yarinya ita ce sanadiyar kubutarmu gaba daya."

Murjanatu da Dan Ali Baba suka amince da junansu. Bayan 'yan kwanaki aka daura musu aure, aka sha biki aka watse, mutanen gari suka yi ta sa albarka, a kan wannan karimci da Ali Baba ya yi wa yarinya Murjanatu, ga ta baiwa amam ya 'yanta ta kuma ya aurar da ita ga dansa, da ma yarinya ce mai ladabi. Duk mutanen gari babu wanda ya san abin da ya faru.

Ali Baba bai kara komawa maboyar 'yan fashin nan ba, domin yana gudun ya hadu da sauran barayin nan biyu da bai san abin da ya same su ba. Da aka shekara ya ga babu wata barazana da barayin nan suka kara yi masa, ran nan sai ya shirya ya faki idon mutane ya dare saman dokinsa, ya nufi dajin. Ya debo dukiyar ya aza kan dokinsa ya hawo ya dawo.

Haka Ali Baba ya ci gaba da zuwa dajin nan daga lokaci zuwa lokaci, yana debo dukiyar da barayin nan suka tara yana kawo wa gida, sai dai duk lokacin da ya je yakan yi sauri ya diba ya dawo don tsoron kada sauran barayin biyu su tarar da shi. Ya ci gaba da yin haka tsawon shekaru, ya kwashe dukiyar duka ya kawo gida, kuma yana ci gaba da kasuwancinsa a kasuwa, don haka babu wanda ya san sirrunsu. Ya zamana babu mai arziki duk fadin kasar kamar Ali Baba.

Yayi zamansa shi da iyalinsa cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai rabawa ta zo ta raba su.

KARSHE.

No comments:

Post a Comment