Thursday 10 July 2014

HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 5

Al'adar garin ce idan mutum ya mutu, 'ya 'yansa ne za su gaji dukan dukiyarsa, idan kuwa ba shi da 'ya 'ya, to 'yan uwansa ne za su gaje shi, idan babu kuma sai matarsa ta gaje shi, idan ba shi da mata sai a saka dukiyarsa a baitulmali.

Bayan mutuwar Kasim, kasancewar ba shi da 'ya 'ya, sai Ali Baba ya gaji dukan dukiyarsa, da gidansa da kuma kuyangar nan tasa mai tsananin hikima, watau Murjanatu. Ali Baba ya kwashe dukan dukiyar da ya samu daga taskar 'yan fashin nan ya koma gidan Kasim tare da matarsa. Ita kuma matar Kasim ta koma gidan mahaifinta.

A cikin wannan halin ne barawon nan ya hilaci dattijo Baba Mustafa har ya kawo shi gidan da Ali Baba ya ke ciki da matarsa da kuyangarsa. Kuma ya yi wa gidan 'yar alama da bakin fenti yadda idan suka dawo cikin dare tare da sauran barayin za su yi saurin shaida gidan.

Bayan barawo ya koma wurin 'yan uwansa, cike da farin cikin gane gidan Ali Bab, ya shaida musu cewa bukata ta biya. Barayi suka yi murna da wannan labari. Babban su ya ce, "Kowa ya zauna cikin shiri, domin yau cikin dare za mu tafi mu kashe wannan mutum, sannan mu kwashe dukan dukiyar da muka samu a cikin gidansa." Barayi duka suka shirya suna jiran dare ya yi.

Ashe kuma bayan tafiyar barawo da Baba Mustafa daga kofar gidan Ali Baba, Murjanatu ta fito domin ta kai sako wani gida. Bayan ta dawo, har za ta shiga gida, sai ta kyalla ido ta ga an yi wata 'yar alama da bakin fenti a jikin kofar gidansu. Ta duba kofar makwabtansu ba ta ga irin wannan alama ba. Ta kuma duba wani gidan, ba ta ga wannan alama ba, ta sa hannu wai ta goge alamar, amma ta ki goguwa. Sai jikinta ya ba ta lalle wannan alama da aka zana a kofar gidansu akwai wata manufa a ciki, ruwa ba ya tsami banza.

Murjanatu ta shiga gida ta samo bakin fenti, ta bi dukkan kofofin gidajen makwabtansu ta yi musu irin 'yar alamar da ta gani a kofar gidansu. Ta ja bakinta ta tsuke, ba ta fada wa kowa ba.

A cikin daji kuwa, barayi sun shirya tsab domin tunkarar gidan Ali Baba, Da lokaci ya yi, suka shirya suka nufo gari. Da suka iso bakin gari, sai suka dakata sai da dare ya raba tsakiya, ba a jin motsin komai a cikin garin, sannan suka shiga.

Barawon da ya gane gidan yana gaba suna biye da shi har suka iso unguwar da gidan Ali Baba ya ke ciki. Da zuwansu, sai suka shiga haska fitulu a kofar gidajen domin gano gidan da barawo ya yi wa lamba. Can sai wani daga cikinsu ya ce, "Ga alamar nan a jikin kofar wancan gidan." Wani kuma ya ce, "A'a, ga gidan nan." Can sai kuma wani ya kyalla ido ya ga alamar a jikin kofar wani gidan dabam.

Da barayin nan suka duba da kyau, sai suka ga ashe duka gidajen unguwar an yi musu lamba. Sai shugaban 'yan fashi ya dubi barawon da suka aiko ya ce, "Sai ka nuna mana gidan da ka gano."

Barawo cikin kaduwa ya ce, "Wallahi ni gida guda na yi wa lamba, ban san me ke faruwa ba."

Shugaban barayi ya ce, "Wane ne daga cikinsu ka yi wa lamba?"

Barawo ya duba, ya kara dubawa, ya kasa gane gidan da Baba Mustafa ya nuna masa. Sai ya ce, "Wallahi ba zan iya shaida shi ba a halin yanzu."

Shugaban barayi ya fusata ya ce, "Ka san ba za ka iya gane gidan ba ka sa muka zo, muka yi wahalar banza, za mu koma a banza a wofi? Lalle hukunci zai hau kanka." Ya ba da umurni aka daure wannan barawo a kan dokinsa, suka kora shi suka nufi cikin daji, wurin maboyarsu.

Da suka isa wurin da dutse ya ke, suka bude shi suka shiga daga ciki. Shugaban 'yan fashi ya sa takobinsa ya dauke kan barawon nan da ya kasa gane gidan Ali Baba. Sannan ya juyo ga sauran barayi ya ce,"Wa zai faranta mini rai, ya shiga cikin gari ya gano mana gidan mutumin nan, ni kuwa in saka masa da abinda duk ya ke bukata?"

Duk barayin nan suka yi jim, can sai wani ya yunkuro daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma ba zan dawo ba sai na gano takamaiman gidan wannan mutumin, idan kuma ban gane ba na yarda a zartar da hukuncin kisa a kaina, kamar yadda aka yi wa na farko."

Barawo ya yi shiri, ya canja kamanninsa kamar wani mutumin kirki, ya nufi cikin gari. Da ya isa cikin gari, sai ya tasar wa rumfar Baba Mustafa, baduku. Ya same shi zaune yana dinkin wata jakar fata.

Barawo ya yi amfani da dabarar da abokinsa na farko ya yi, ya ja hankalin dattijo da kudi, har ya kai shi dai dai kofar gidan Ali Baba. Bayan da ya sallami dattijon, sai ya dauko jan fenti a cikin jakarsa, ya sami wani wuri a jikin gidan, wanda ba duka idon mutum zai yi saurin kaiwa ga wurin ba, ya yi 'yar alama wadda za ta sa ya gane gidan.

Bayan ya tafi, sai Murjanatu ta fito zuwa wurin da aka aike ta. Bayan ta dawo, kafin ta shiga gida sai kuwa idonta ya kai ga alamar da barawon nan ya yi da jan fenti. Ta tsaya tana tunanin shin wai me ake nufi da wadan nan alamomi da ake yi musu a jikin gida? Ta je ta samo kalar fentin, ta bi dukan gidajen makwabtansu ta yi musu irin wannan 'yar alamar. Ta shiga gida ba ta fada wa kowa ba.

Shi kuwa barawo da ya koma sai ya shaida wa shugabnsu cewa ya gane gidan, don haka su shirya da dare su shiga gari su kashe mai gidan sannan su kwashe dukan dukiyar da suka samu a cikin gidan.

Da lokaci ya yi, barayi suka shirya suka shiga cikin garin da dare, lokacin kuwa duk mutane kowa ya yi barci, suka tasar wa unguwar da Ali Baba ya ke da iyalinsa. Da isarsu sai shugabansu ya ce da barawon nan, "Maza nuna mana gidan mu aikata abin da ya kawo mu, mu juya kafin gari ya waye."

Barawo ya haska fitilarsa a jikin gida na farko, dai dai inda ya san ya yi alama, sai kuwa ga 'yar alamar da jan fenti. Har za su balle gidan su shiga, sai shugabansu ya ce, "Bari mu fara tabbatar wa da kanmu cewa wannan shi ne gidan da muke nema, kada a sami kuskuren da aka samu jiya, ku tafi ku haska sauran gidajen, idan babu wani gida mai irin wannan alama, to wannan shi ne gidan da muke nema."

Sauran barayi suka warwatsu cikin unguwar, duk gidan da suka haska fitilarsu sai su ga irin wannan alama a jiki. Suka zo suka fada wa shugabansu. Shugaban ya tambayi barawon ko zai iya gane gidan a cikin sauran gidajen da suke da alama iri daya? Barawo ya ce ba zai iya ba.

Suka koma maboyarsu. Shi ma wannan barawo aka zartar masa da hukuncin kisa. Da shugabansu ya ga cikin dan kankanin lokaci ya yi asarar mutum biyu daga cikin yaransa, sai ransa ya baci, ya yi fushi, fushi mai tsanani. Ya yi rantsuwa da abin da zai kashe shi cewa, shi da kansa zai shiga gari ya gane ainihin wannan gida da suke nema, wanda ya yi sanadiyyar rasa yaransa biyu. Lalle mai wannan gida zai dandana azaba mai tsanani kafin su kashe shi.

Washe gari shugaban barayi ya yi shiri da kansa ya shiga gari. Ya yi amfani da dabarar da barayin nan biyu suka yi amfani da ita, ta saye dattijo baduku, watau Baba Mustafa da kudi.

Da suka zo kofar gidan, shugaban barayi ya sallami dattijo. Ya dubi gidan da kyau tun daga kasa har bisa, ya yi murmushi ya ce a ransa, "Yaro dai yaro ne, in ba halin yarinta ba mene na abin yi wa wannan gida alama? Wannan makeken dutsen da ya ke kwance gab da kofar shiga gidan ai ya isa alamar da za a gane gidan, ko ba shi ba ma, waccan tsagawar da bangon gidan ya yi ita ma alama ce babba ta gane gidan." Ya sake yin murmushi, ya dubi gidan ya ce, "Mai gidan nan yau kwananka ya kare, Allah ya kai mu dare." Ya koma gun 'yan uwansa.

Da Murjanatu ta fito daga gida, bayan tafiyar shugaban barayi, ta tsaya ta duba jikin gidansu da kyau ko za ta ga wata sabuwar alama, amma ba ta gani ba. Ta ce a ranta, "Wata kila mai yi musu lamba a jikin gida ya gaji ya watsar, ko wane ne? Oho! Wata kila ma yara ne." Ta kama harakokin gabanta, ba ta koma kan batun ba.

Za mu ci gaba....

No comments:

Post a Comment